Sport
Dollar
40,2573
-0.02 %Euro
46,8058
-0.36 %Gram Gold
4.322,7100
-0.22 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Manhajoji cikin gida masu aiki da fasahar Kirkirarriyar Basira na bayar da kyakkyawar damar musayar bayanai, in ji Shugaban Hukumar Masana’antun Tsaro na Turkiyya.
An kera garkuwar makamai masu linzami ta Turkiyya mai shigifai da yawa ta "Steel Dome" gaba ɗaya da kayayyaki tare da amfani da fasahar kere-kere ta cikin gida kuma tana aiki da Kirkirarriyar Basira.
Shugaban Hukumar Kula da Masana’antun Tsaro na Turkiyya (SSB) ya ce an samar da Steel Dome ne don gano wa kawar da barazanar da ta taso daga kusa da ta nesa, inda take aiki da tsaro mai shigifofi amma tana tsaron aikin bai daya.
Ya yi jawabi ne a wajen wani taro da kamfanin SAHA suka shirya a Istanbul.
Gorgun ya kara da cewa tsarin tsaron na sama na dauke da matakan shigifofi da suka hada da Siper, Hisar A+ da O+, tsarin Korkut da Sungur da suke aiki karkashin umarnin na’urorin radar, maganaɗisun lantarki masu idanu, siginoni da babban tsarin hasken laser.
Tsarin kula da bayar da umarni na Steel Dome na aiki da fasahar Kirkirarriyar Basira, wanda ke bayar da kai dauki yadda ya kamata da isasar da sakonni ga sauran cibiyoyin da ake aiki da su.
“Gudunmawar Kirkirarriyar Basira a ayyukan anke hukunci na taka muhimmiyar rawa wajen hanzari da kuma aiki yadda ake so, tare da daukar matakan ‘yan’adam,” in ji shi.
“Da a ce mun sayi Steel Dome maimakon mu kera da kan mu, da wannan musayar bayanai tsakanin na’urorin aiki ya zama babbar matsalar injiniyanci.”
Gorgun ya yi tsokaci da cewa sama da rabin kayan tsaron Turkiyya da ake fitarwa zuwa kasashen waje na tafiya kasashen NATO da Turai, kuma an samar da sashe na musamman da yake kula da alakar tsaron NATO da Turkiyya.
Comments
No comments Yet
Comment