Dollar

38,5992

0.33 %

Euro

43,6545

0.2 %

Gram Gold

4.017,2800

0.33 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ministocin Harkokin Wajen Turkiyya da Aljeriya sun shugabancin taron Shiri na Hadin Gwiwa Tsakanin Turkiyya da Aljeriya.

Aljeriya na son ƙulla kasuwancin dala biliyan 10 da Turkiyya

Ministan Harkokin Wajen Aljeriya Ahmed Attaf ya ce kasar na da manufar kara yawan kasuwancin da take yi da Turkiyya zuwa dala biliyan 10, bayan ganawar sa da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan.

Ministocin Harkokin Wajen Turkiyya da Aljeriya sun shugabancin taron Shiri na Hadin Gwiwa Tsakanin Turkiyya da Aljeriya Karo na Uku da aka gudanar a Algiers, a ranar Litinin.

A yayin ganawar, Attaf ya yi karin haske kan sakamakon da ake samu a alakar Aljeriya da Turkiyya da ta karfafa bisa umarnin Shugaban Kasar Aljeriya Abdelmajed Tebboune da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

A shekarar da ta gabata, ya ce kasuwancin kasashen biyu ya kai dala biliyan 6, mataki mai muhimmanci, kuma bisa umarnin shugabannin kasashen biyu, suna da manufar habaka kasuwancin zuwa dala biliyan 10.

Attaf ya jaddada muhimmancin magance matsalolin da ake samu wajen cim ma manufofi masu kyau, yana mai cewa tattalin arzikin Aljeriya na ci gaba da samar damarmakin zuba jari a bangarori da dama, ciki har da makamashi mai sabuntuwa, masana’antun samar da magunguna, da fadada hadin kai da aiki tare.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#