Sport
Dollar
38,5992
0.33 %Euro
43,6545
0.2 %Gram Gold
4.017,2800
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Bankin ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce za a samar da dala biliyan 2.95 tsawon shekara huɗu a wannan shirin, inda zai samu ƙarin kimanin dala biliyan 3.21 daga sauran ƙawayen kawo ci gaba.
Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB) ya ware dala miliyan 650 a duk shekara tun daga 2025 zuwa 2030 domin wani shiri na musamman na haɓaka ci gaban tattalin arziki a Nijeriya.
Bankin ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce za a samar da dala biliyan 2.95 tsawon shekara huɗu a wannan shirin, inda zai samu ƙarin kimanin dala biliyan 3.21 daga sauran ƙawayen kawo ci gaba.
Sanarwar ta ce shirin zai mayar da hankali kan abubuwa biyu muhimmai waɗanda suka haɗa da kawo ci gaba ma ɗorewa da samar da ababen more rayuwa waɗanda suka zo daidai da tsarin da ake da shi na sauyin yanayi da samar da gasa da ci gaban masana'antu; da kuma samar da daidaito a tsakanin matasa da jinsi ta ɓangaren ci gaban masana’antu.
A cewar bankin, dabarun na da nufin cike giɓin da ake da shi a ɓangaren ababen more rayuwa a Nijeriya - wanda aka ƙiyasta ya kai dala tiriliyan 2.3 tsakanin shekarar 2020 zuwa 2043 - ta hanyar saka hannun jari a hanyoyin da suka dace da yanayi, fadada wutar lantarki, tsaftar ruwan sha, da tallafa wa harkokin noma da ke samar da ayyukan yi, musamman ga mata da matasa.
Ana sa ran zuba jarin zai tallafa wa Nijeriya wurin ninka girman tattalin arzikinta zuwa dala tiriliyan ɗaya da kuma samar da ayyukan yi kusan fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar.
Comments
No comments Yet
Comment