Dollar

43,4015

-0.01 %

Euro

51,8032

-0.88 %

Gram Gold

7.398,9100

2.41 %

Quarter Gold

12.428,8800

3.99 %

Silver

158,7600

1.47 %

An kammala bincike, za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotun soji

Rundunar Sojin Nijeriya Za Ta Gurfanar da Wasu Jami’anta kan Zargin Yunƙurin Juyin Mulki

Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da cewa za ta gurfanar da wasu jami’anta a gaban kotun soji bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, lamarin da ta ce ya saɓa wa dokokin soji da tsarin aiki. (TRT Hausa)

A wata sanarwa da Daraktan Watsa Labarai na Hedkwatar Tsaron Nijeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya fitar ranar Litinin, rundunar ta ce za a tuhumi sojojin da abin ya shafa kamar yadda dokar soji da sauran dokokin ƙasar suka tanada. (TRT Hausa)

Sanarwar ta tunatar da cewa a watan Oktoban 2025 an kama sojoji 16 bisa zargin rashin ɗa’a da keta dokokin aiki, inda aka kammala bincike tare da miƙa rahoto ga manyan jami’ai kamar yadda doka ta buƙata. (TRT Hausa)

Ta ƙara da cewa cikakken binciken da aka gudanar ya yi nazari dalla-dalla kan dukkan batutuwan da suka shafi lamarin, kuma ya gano wasu sojoji da ake zargi sun yi yunƙurin kifar da gwamnati, abin da ya saba wa ƙa’idoji da dokokin rundunar. (TRT Hausa)

Rundunar ta ce duk sojojin da ake da alamar tambaya a kansu za su gurfana a gaban kotun soji domin fuskantar tuhuma, tana mai jaddada cewa za a ɗauki matakan ne bisa ƙa’ida da adalci. (TRT Hausa)

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#