Dollar

43,4099

0 %

Euro

51,7411

-0.98 %

Gram Gold

7.379,2400

2.14 %

Quarter Gold

12.428,8800

3.99 %

Silver

157,8400

0.88 %

An ceto su a yankin iyakar Zango yayin ƙoƙarin safararsu zuwa Libya da Turai

Hukumar Shige da Fice Ta Ceto Mutum 22 daga Masu Safarar Mutane a Katsina

Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) a Daura ta ceto mutum 22 daga hannun masu safarar mutane a yankin iyakar Zango na Jihar Katsina, bayan samun bayanan sirri daga al’ummomin kan iyaka kan zirga-zirgar da ake yi ba bisa ƙa’ida ba. (TRT Hausa)

Kwamandan rundunar NIS a kan iyakar Jibia, Haruna Zakirai, ya ce jami’an hukumar tare da ‘yan sandan Daura sun kai ɗauki cikin gaggawa, inda suka ceto mutanen a wani gini da ba a kammala ba a ƙauyen Maibara da ke ƙaramar hukumar Zango. (TRT Hausa)

A cewarsa, waɗanda aka ceto sun haɗa da mata 11 da maza 11 masu shekaru tsakanin 17 zuwa 35, daga jihohi daban-daban na Nijeriya ciki har da Legas, Osun, Rivers, Kwara, Katsina, Imo, Ondo, Benue da Babban Birnin Tarayya Abuja. (TRT Hausa)

Binciken farko ya nuna cewa ana shirin safarar mutanen ta hanyoyi marasa tsari zuwa Libya, daga nan kuma zuwa Turai, inda aka yaudare su da alkawarin samun damar tattalin arziki mai kyau. (TRT Hausa)

Zakirai ya ce wani ɗan ƙasar Togo na cikin waɗanda aka ceto kuma za a mayar da shi ƙasarsa bayan kammala bincike, yayin da babban jagoran masu safarar da aka fi sani da “Cargo” ya tsere kuma ana nemansa ruwa-a-jallo. (TRT Hausa)

Hukumar Shige da Fice ta sake jaddada ƙudirinta na yaƙi da safarar mutane da shige da fice ba bisa ƙa’ida ba, tare da kira ga jama’a da su bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai kan masu aikata irin waɗannan laifuka. (TRT Hausa)

 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#