Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaba Tinubu ya kuma gabatar da wani kudiri da ke neman gyara Dokar Babbar Kotun Tarayya don ƙara yawan alkalai daga 70 zuwa 90, daga tanadin farko na 50.

Tinubu ya nemi a ƙara yawan alkalan Kotunan Ɗaukaka Ƙara da na Tarayya a Nijeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya aika da buƙatu da dama na gyara a fannin shari'ar ƙasar ga Majalisar Dattawa, inda shugaban ya nemi a ƙara yawan alkalai a manyan kotuna a faɗin ƙasar.

A yayin zaman majalisar na ranar Talata, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya karanta wata wasiƙa daga Shugaba Tinubu wadda ta nemi a yi wa Dokar Ɗaukaka Ƙara kwaskwarima don ƙara yawan alkalai daga 70 zuwa 110.

Shugaban ya ce matakin yana da nufin ƙarfafa ayyukan kotunan da kuma rage yawan shari'o'in da ake samu.

Kazalika Shugaba Tinubu ya kuma gabatar da wani ƙudiri da ke neman gyara Dokar Babban Kotun Tarayya don ƙara yawan alkalai daga 70 zuwa 90, daga tanadin farko na 50.

Sannan shugaban ya roƙi Majalisar da ta gaggauta yin la'akari da ƙudurorin da aka gabatar wadda aka aika zuwa ga Kwamitin Dokoki da Kasuwanci na Majalisar Dattawa don nazari da kuma ɗaukar matakin doka ta gaba.

Haka kuma, shugaban ya roƙi Majalisar da ta tabbatar da naɗin Mai Shari'a Oyewole Joseph Kayode a matsayin Alkalin Kotun Koli ta Nijeriya.

Majalisar Dattawa ta kuma karɓi wani ƙudiri da aka yi wa kwaskwarima na Kotun Daukaka Kara, wanda ya gabatar da shawarar kafa Cibiyar Magance Rikici ta (ADR) don sauƙaƙa tsarin wasu shari'o'in kotuna.

An kuma tura wannan kudiri ga Kwamitin Dokoki da Kasuwanci na majalisar.

A bangare guda kuma, Shugaban ya kuma aika da wata buƙata ta neman a yi wa kudirorin sashen lafiya 24 kwaskwarima domin magance matsalolin da suka shafi yawan membobin hukumar.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#