Dollar

42,9494

0.04 %

Euro

50,5776

0.01 %

Gram Gold

6.053,0600

1.16 %

Quarter Gold

10.158,3000

0.93 %

Silver

104,2300

3.63 %

Kawo yanzu ba a san abin da ya yi sanadin fashewar ba, amma an soma gudanar da bincike, in ji shi.

Wani abu ya fashe a Babban Asibiti a Jihar Kebbi ta Nijeriya

Rundunar 'yansandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da fashewar wasu abubuwa a babban asibitin ƙaramar hukumar Bagudo da sanyin safiyar Talata.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yansandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman Anisma, a wata sanarwa ya ce tawagar ƙwararru ta EOD-CBRN ta isa wajen don gudanar da cikakken bincike kan halin da ake ciki a asibitin.

Ya kuma tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata, amma wani gini a sashen gidajen ma'aikata na asibitin ya lalace, yayin da aka kwashe mutanen da ke cikinsa ba tare da matsala ba.

Kawo yanzu ba a san abin da ya yi sanadin fashewar ba, amma an soma gudanar da bincike, in ji shi.

Sai dai SP Usman ya ce Kwamishinan 'yansandan Jihar ya tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin dominn tabbatar da zaman lafiya.

'Yansanda sun buƙaci jama'a da su kwantar da hankalinsu su guji kusantar wajen don nuna goyon baya ga ayyukan tsaro da bincike da ake gudanarwa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#