Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Turkiyya ta ɗauki alƙawarin ƙarfafa diflomasiyya a duniya yayin da Shugaba Erdogan ya jaddada buƙatar samar da mafita ta haɗa kai da ci-gaba da tallafa wa yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni a taron Turkmenistan .
Turkiyya ta jajirce wajen samar da zaman lafiya da tattaunawa, kamar yadda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana ranar Jumma’a a wani taron ƙasa da ƙasa a Turkmenistan.
Da yake magana a taron ƙasa da ƙasa na zaman lafiya da amincewa a Ashgabat, Erdogan ya ce Ankara tana aiki “da dukkan ƙarfinmu” domin tabbatar da cewa diflomasiyya ce take kan-gaba, inda za ta yi amfani da nauyin da ya rataya a a kanta sakamakon tarihi da al’ada da kuma inda ƙasar take a duniya.
“A matsayin Turkiyya, muna aiki da dukkan ƙarfinmu —ƙarƙashin jagorancin nauyin tarihinmu da inda muke a duniya da al’adarmu suka ɗora mana a kai—domin tabbatar da cewa zaman lafiya da tattaunawa ne a kan-gaba,” kamar yadda Erdogan ya bayyana.
Ya kuma ƙara da cewa Turkiyya a shirye take ta tallafa wa ƙoƙarin domin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta da zaman lafiya mai ɗorewa, ciki har da shirye-shirye da suka shafi rikicin Rasha da Yukrain.
Da ya juya Gabas Ta tsakiya kuma, Erdogan ya jaddada cewa duka wani shirin samar da zaman lafiya dole ya haɗa da Falasɗinawa ya kuma samar da mafita ta ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.
Ya kuma yi gargadin cewa har yanzu yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Oktoba tsakanin Isra’ila da Hamas a Gaza na da rauni kuma ya yi kira da ƙasashen duniya su ci gaba da mara mata baya domin ɗorewarta.
Kasancewar Turkmenistan ‘ya babu ruwanta ta dindindin
Shugaba Erdogan ya halarci wani bikin ajiye fure a wurin tunawa da manufa ta babu ruwanmu ta Turkmenistan yayin da shugabannin duniya suka taru a Ashgabat.
Erdogan ya haɗu sauran shugabannin ƙasashen duniya da aka gayyata, ciki har da Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Iran Masoud Pezeshkian.
Daga baya Erdogan ya halarci wani wuri na ɗaukar hoton iyali bayan bikin maraba a hukumance a wurin taron.
Shugabannin za su halarci zaman farko na taron daga baya.
Taron a Ashgabat ana yin shi ne domin ciki shekara 30 da ƙasar ta zama ‘yar babu ruwanta ta dindindin da kuma yadda zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana shekarar 2025 a matsayin “shekarar zaman lafiya da amince ta duniya.”
Comments
No comments Yet
Comment