Dollar

38,7974

0.05 %

Euro

43,1060

0.11 %

Gram Gold

4.035,2800

0 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Duk da fama da hauhawar farashin kayayyaki da ƙasar ke yi, tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka, a cewar wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar.

Tattalin arzikin Nijeriya ya habaka a yayin da ake fama da hauhawar farashi, in ji Bankin Duniya

Tattalin arzikin Nijeriya ya samu haɓaka a kusan shekaru goma a 2024, inda a watanni uku na karshen 2024 aka samu haɓaka sosai, in ji Bankin Duniya a ranar Litinin, amma ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashi na ci gaba da zama ƙalubale.

Manyan matakan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ke ɗauka, ciki har da kawo karshen tallafin mai, da janye tallafi kan wutar lantarki da karya darajar naira har sau biyu, sun ƙara matsa lamba ga farashin kayayyaki.

Babban jami’in tattalin arzaki na Bankin Duniya a Nijeriya, Alex Sienaert, ya bayyana a yayin fitar da rahoto a Abuja cewa tattalin arzikin ya ƙaru da kashi 4.6 a watanni uku na ƙarshen 2024, inda ya kuma yi nuni da cewa zai ci gaba da haɓaka a farkon 2025.

Bankin Duniya na sa ran tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka a wannan shekarar da kashi 3.6.

Sienaert ya ce harajin gwamnati ya ƙaru da kashi 4.5 sama da na shekarar da ta gabata, wanda “muhimmiyar nasara” ce, da janye tallafi ga kuɗaɗen ƙasashen waje, da kyautata tsarin karɓar haraji da yawan saka kuɗaɗe a asusun gwamnati suka kawo.

Kuɗaɗen shiga masu yawa da aka samu sun taimaka wajen cike giɓin kasafin kudi da aka yi hasashen ya kai kusan kashi uku a 2024, daga kashi 5.4 da aka samu a 2023.

Amma duk da haka, Nijeriya na ci gaba da fama da hauhawar farashi, inda Sieneart ya yi gargaɗin cewa dole ne a dɗki matakan tsuke bakin aljihu da tasarrufin kuɗaɗe bisa doka da oda.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#