Rundunar ta ce ’yanta’addan sun kai hari da adadi mai yawa kan dakarun Bataliyar Sojojin Musamman ta 101 daga bangarori huɗu daban-daban.
Rundunar Sojin Nijeriya ta ce dakarun Operation HADIN KAI sun dakile wani hari da ’yan ta’addan DAESH suka kai ta fuskoki daban-daban a Kukawa, Jihar Borno, inda suka kashe sama da ’yanta’adda 25 tare da ƙwato makamai da alburusai.
Rundunar ta ce ’yanta’addan sun kai hari da adadi mai yawa kan dakarun Bataliyar Sojojin Musamman ta 101 daga bangarori huɗu daban-daban.
Sai dai sojojin sun mayar da martani mai ƙarfi ta hanyar amfani da karfin makamai, dabarun yaƙi da ingantaccen haɗin gwiwa a fagen daga.
Rundunar ta ce wasu jajirtattun sojoji sun rasa rayukansu yayin arangamar.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce dakarun, tare da tallafin rundunar sojin sama, sun fatattaki ’yan ta’addan, inda suka kashe da dama tare da tilasta wa waɗanda suka tsira tserewa cikin rudani.
Sanarwar ta ce binciken farko ya nuna cewa an kashe sama da ’yan ta’adda 25, yayin da aka gano gawarwakin 14 zuwa yanzu.
A yayin ci gaba da binciken yankin, sojojin sun kwato tarin makamai da alburusai, ciki har da bindigogin AK-47 guda shida.
Rundunar ta ce ana ci gaba da binciken yankin domin kwato wasu ƙarin makamai, bibiyar ’yan ta’addan da suka tsere da kuma hana su sake haɗuwa.
Rundunar Sojin Nijeriya ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan sojojin da suka rasa rayukansu, tare da bayyana cewa jarumtakarsu, sadaukarwarsu da kishin aikinsu za su ci gaba da zama abin tunawa a tarihin hidimarsu ga ƙasa.
Rundunar ta ce fatattakar harin ya nuna shirin yaƙi, juriya da ƙwarewar dakarun Sojin Nijeriya a fagen yaƙi na Arewa maso Gabas.
Ta ƙara da cewa hakan ya kuma nuna ƙara inganta haɗin gwiwar sojojin sama da na ƙasa, da kuma ayyukan haɗin gwiwa wajen dakile ayyukan ’yan ta’adda da hana su ’yancin gudanar da ayyukansu.
Rundunar ta sake jaddada ƙudirinta na ci gaba da matsa lamba kan ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.
Ta ce dakarunta za su ci gaba da gudanar da sintiri mai ƙarfi, ayyukan leƙen asiri da kuma hare-haren haɗin gwiwa tare da sauran rundunonin tsaro domin tarwatsa hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda, kare al’umma da kuma tabbatar da tsaron ƙasa.

