Shugabannin ’yanbindiga biyu na cikin waɗanda aka kashe a musayar wuta a Danmusa

Sojoji sun kashe ’yanbindiga 45 a Katsina

Dakarun Sojojin Nijeriya sun kashe wasu da ake zargin ’yanbindiga ne guda 45 a wata musayar wuta da ta faru a Ƙaramar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina.

Majiyoyin tsaro sun ce farmakin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu kan motsin ’yanbindiga da ake zargin suna aiki a wasu sassan Katsina da kuma maƙwabciyarta Jihar Zamfara.

Daga cikin waɗanda aka kashe akwai wasu manyan shugabannin ’yanbindiga biyu da suka haɗa da Alti, wanda ake cewa ɗan’uwa ne kuma mataimaki ga ƙasurgumin shugaban ’yanbindiga Adamu Alieru, da kuma wani kwamanda da ake kira Damale.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne bayan wasu ’yanbindiga a kan babura dauke da manyan makamai sun kai hari ƙauyen Alhazawa da ke Ƙaramar Hukumar Musawa a ranar 5 ga Maris, inda suka kwashe shanun mazauna yankin.

Sai dai al’ummar yankin tare da wasu ’yanbindiga da suka tuba sun yi turjiya ga harin, inda suka kashe ’yanbindiga huɗu tare da ƙwato shanun da aka sace sannan suka mayar wa masu su.

A cewar majiyoyin, ’yanbindigar sun sake haɗuwa a ranar 6 ga Maris domin kai wani harin ramuwar gayya. Amma yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Musawa ta cikin Maidabino A Ward, sun ci karo da dakarun sojoji da ke sansanin Forward Operating Base (FOB) da ke Dan Ali a Ƙaramar Hukumar Danmusa.

Hakan ya janyo wata mummunar musayar wuta inda sojojin suka yi nasarar rinjayar ’yanbindigar tare da kashe 45 daga cikinsu.

Sai dai an samu asara a ɓangaren sojoji, inda sojoji uku suka rasa rayukansu yayin fafatawar.

Bincike ya nuna cewa Alti ya ƙara fitowa fili a ayyukan ’yanbindiga bayan mutuwar ɗan’uwansa Kachalla Dan Isihu, wanda jami’an tsaro suka kashe a wani hari da suka kai kan ’yanbindiga a baya.

An ce Alti yana daga cikin waɗanda ke tsara hare-hare a kan al’ummomi musamman a yankin Danjibga na Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Majiyoyin tsaro sun ce dakarun sojoji sun ƙara tsaurara bincike a yankin domin bin diddigin sauran ’yanbindigar da suka tsere tare da lalata cibiyoyin ayyukansu.

Tushen labari: Newstimehub

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#