Janar Waidi Shaibu ya bukaci sojoji su ƙara ƙaimi a aikin leken asiri domin gano ’yan bindiga

Babban Hafsan Sojin Kasa ya umarci a ƙara ƙoƙari wajen ceto ɗaliban Kebbi

Babban Hafsan Sojin Kasa na Nijeriya (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya umarci dakarun soji da ke ƙarƙashin rundunar Operation FANSAN YANMA da su ƙara ƙoƙari wajen ceto ɗaliban da aka sace daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi.

Janar Waidi Shaibu ya bayar da umarnin ne a ranar Litinin, 17 ga Nuwamban 2025, yayin wata ziyarar aiki da ya kai jihar Kebbi, kwana guda bayan harin da ’yan bindiga suka kai makarantar.

Yayin da yake jawabi ga kwamandoji da sojojin da ke aiki a yankin, Babban Hafsan Sojin ya bukace su da su ƙara himma wajen tattara bayanan sirri da kuma bin diddigin maharan da suka sace ɗaliban.

“Dole ne mu nemo waɗannan yaran. Ku yi aiki cikin hikima da ƙwarewa kan duk wani bayanin sirri,” in ji Janar Shaibu, yana mai jaddada cewa babu wani zaɓi face samun nasara a aikin ceton.

A yayin ziyarar, Janar Shaibu ya kuma gana da ’yan banga da mafarauta na yankin, inda ya bayyana su a matsayin muhimman abokan aiki a ƙoƙarin da ake yi na dawo da tsaro.

Ya ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da aiki kafada da kafada da jami’an soji tare da amfani da iliminsu na yankin domin taimakawa wajen gano maharan.

Babban Hafsan Sojin ya kuma jaddada cewa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma zai taimaka wajen maido da zaman lafiya da tabbatar da cewa ɗalibai za su ci gaba da zuwa makaranta ba tare da tsoro ba.

Tushen labari: Newstimehub

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#