Dollar

39,0330

0.28 %

Euro

44,0488

-0.01 %

Gram Gold

4.140,4200

0.42 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Turkiyya da Siriya sun yi nazari kan sabunta alaƙa yayin da jami'in leen asirin Turkiyya ke ziyara a Damascus, inda suka tattauna batun tsaro kan iyakokin kasar, da kwance ɗamarar kungiyoyin 'yan ta'adda, da komaw 'yan gudun hijira gida.

Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Turkiyya ya gana da shugaban Syria Al Sharaa kan tsaron yankin

Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa ta Turkiyya (MIT), İbrahim Kalin, ya gudanar da wata muhimmiyar ganawa a birnin Damascus tare da Shugaban Siriya Ahmed al Sharaa da Ministan Harkokin Waje Asaad al Shaibani, da shugaban leƙen asiri Hussein al Salama, kamar yadda majiyoyi da suka san da ziyarar suka bayyana.

Tattaunawar, wadda ta ɗauki awanni da dama a ranar Talata, ta fi mayar da hankali kan dawo da dangantakar ƙasashen biyu da kuma tabbatar da zaman lafiya a Siriya bayan shekaru na yaƙin basasa.

Kalin ya jaddada girmamawar Turkiyya ga cikakken yankin Siriya da ikon siyasarta, tare da tabbatar da shirye-shiryen Ankara na tallafa wa Damascus wajen dawo da doka da oda da kuma sake gina cibiyoyin gwamnati, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.

“Turkiyya ta jajirce wajen tabbatar da haɗin-kan Siriya da kuma ɗorewar zaman lafiya,” in ji Kalin kamar yadda jami’an Turkiyya suka bayyana.

Harkokin Yaƙi da Ta’addanci da Tsaron Iyaka

Babban jigon tattaunawar shi ne haɗin gwiwar tsaro. Rahotanni sun nuna cewa ɓangarorin biyu sun tattauna kan ƙwace makamai da kuma sake haɗa ƙungiyoyin da suka ɗauki makamai, musamman ƙungiyar ta’addanci ta PKK/YPG, cikin sabon tsarin Siriya.

Jami’an Turkiyya sun sake jaddada damuwarsu kan ayyukan ta’addanci kusa da iyaka, tare da nuna muhimmancin tabbatar da tsaron iyakokin ƙasashen biyu.

Haka kuma, an tattauna batun miƙa gidajen yari da sansanonin tsare waɗanda ke da alaƙa da Daesh ga hukumomin Siriya, wani mataki da Ankara ke ganin yana da muhimmanci wajen tabbatar da tsaron yankin na dogon lokaci.

Tattaunawar ta kuma shafi batutuwan dabarun tsaro na gaba ɗaya, ciki har da sarrafa iyakoki, sake buɗe manyan ƙofofin kwastam, da kuma sake gina hanyoyin kasuwanci. Türkiye ta bayyana shirinta na taimakawa Damascus wajen dawo da waɗannan muhimman wuraren da yaƙin ya lalata.

Ci gaban Yanki a Kan Tattaunawa

Kalin da shugabannin Siriya sun kuma tattauna kan rikice-rikicen yankin da ke ci gaba, ciki har da hare-haren sama na Isra’ila da ke ƙaruwa a kan yankin Siriya da kuma take dokokin sararin samaniya da take yawan yi.

An kuma tattauna batun dage takunkumin ƙasa da ƙasa kan Siriya, tare da ci gaba da yaƙi da ragowar ƙungiyar ta’addanci ta Daesh, waɗanda suka kasance manyan batutuwa a ajandar.

Wani muhimmin batu shi ne dawo da ‘yan gudun hijirar Siriya cikin yardar rai da kuma cikin aminci.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an Turkiyya sun bayyana sha’awar Ankara na yin aiki tare da Dimashƙu kan dabaru da tabbacin tsaro da ake buƙata don sauƙaƙe dawowar su.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#