Sport
Dollar
38,8949
0.36 %Euro
43,4533
-0.25 %Gram Gold
3.997,1000
-0.9 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A ɗaya daga cikin shawarwarin yarjejeniyar da ake son cimmawa, Amurka za ta saki biliyoyin daloli ga Libya waɗanda tun can dama kuɗin na Libiya ne amma Amurkar ta riƙe su fiye da shekaru goma.
Gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump na shirin tilasta wa Falasɗinawa fiye da miliyan guda daga Gaza yin hijira zuwa ƙasar Libya, kamar yadda wasu mutum biyar da ke da masaniya kan shirin suka shaida wa kafar watsa labarai ta NBC.
Duk da cewa babu cikakkun bayanai game da shirin kuma ba a kammala cim ma matsaya ba, amma a halin yanzu ana ci gaba da mayar da muhimmanci kan shirin kuma rahotanni sun nuna cewa tuni gwamnati Amurka ta tuntuɓi gwamnatin Libya.
A ɗaya daga cikin shawarwarin yarjejeniyar da ake son cimmawa, Amurka za ta saki biliyoyin daloli ga Libya waɗanda tun can dama kuɗin na Libiya ne amma Amurkar ta riƙe su fiye da shekaru goma.
Majiyoyin sun ce ana bai wa Isra’ila bayanai kan halin da ake ciki a tattaunawar duk da cewa babu ƙarin bayani kan irin tasirin da Isra’ila ke da shi a wannan shiri.
Basem Naim, wanda babban jami’i ne na Hamas, ya ce ƙungiyarsu ba ta da wata masaniya game da shirin da ake yi na korar Falasɗinawa zuwa Libya.
Comments
No comments Yet
Comment