Rahotanni sun ce ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi ya mutu a harin da ba a fayyace ba

An Kashe Saif al-Islam Gaddafi a Libya

An kashe Saif al-Islam Gaddafi, ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi mai shekara 53, kamar yadda lauyansa Khaled el-Zaydi da wasu majiyoyi da ke kusa da iyalinsa suka tabbatar, tare da rahotannin kafofin watsa labaran Libya. TRT Hausa

Mai ba shi shawara, Abdullah Osman, ya tabbatar da mutuwarsa a ranar Talata, sai dai hukumomin Libya har yanzu ba su fitar da sanarwar hukuma da ke tabbatar da lamarin ba. TRT Hausa

Kafofin watsa labaran Libya sun rawaito cewa an kashe Saif al-Islam ne a gidansa, inda wasu mutane huɗu da ba a tantance su ba suka kai harin, bayan sun lalata na’urorin kyamarorin sa ido da ke wurin. TRT Hausa

Ofishin babban lauyan Libya ya ce ya fara bincike kan kisan, yayin da bayanai ke ci gaba da kasancewa masu ruɗani sakamakon rashin cikakken bayani daga hukumomi. TRT Hausa

A shafinsa na Facebook, Moussa Ibrahim, tsohon mai magana da yawun gwamnatin Gaddafi, ya zargi makiyan Libya da kashe Saif al-Islam, yana mai cewa an kashe “fata da makomar ƙasa” tare da ƙara rarraba al’ummar Libya. TRT Hausa

Kungiyar soji ta “Brigade 444” da ke da alaƙa da ma’aikatar tsaron gwamnatin haɗin kan ƙasa ta musanta alaƙa da arangamar da aka ruwaito a Zintan da kuma labarin kisan Saif al-Islam. TRT Hausa

Tun bayan juyin juya halin 2011 da ya kifar da mulkin mahaifinsa, Saif al-Islam ya kasance a Zintan, amma bayan an sake shi a 2017, ba a san inda yake ba har zuwa wannan rahoto na mutuwarsa. TRT Hausa


 

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#