Yarjejeniyar za ta ƙarfafa hulɗar kasuwanci da diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu

Ghana da Zambia sun amince da tafiya babu biza

Ghana da Zambia sun ƙulla wata yarjejeniya da ta bai wa ‘yan ƙasashen biyu damar shiga ƙasashen juna ba tare da buƙatar biza ba. Ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki ta kwana uku da Shugaba John Dramani Mahama ya kai Zambia domin ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da tattalin arziki. TRT Hausa

Shugaba Mahama ya isa birnin Lusaka ranar Laraba, inda Shugaban Zambia Hakainde Hichilema ya tarbe shi a filin jirgin saman Kenneth Kaunda na ƙasa da ƙasa. Ziyarar na da nufin ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnatoci da al’ummomin ƙasashen biyu. TRT Hausa

Ministan harkokin wajen Ghana ya bayyana ɗauke buƙatar bizar a matsayin babban mataki a tarihin dangantakar Ghana da Zambia, yana mai cewa hakan zai sauƙaƙa tafiye-tafiye tare da buɗe damammaki a fannoni kamar cinikayya, yawon buɗe ido, zuba jari da musayar al’adu. TRT Hausa

A cewarsa, matakin ya zo ne bisa umarnin Shugaba Mahama kai tsaye, domin rage ƙalubalen da ‘yan ƙasashen biyu ke fuskanta wajen samun biza, musamman ɗalibai, ‘yan kasuwa da masu yawon buɗe ido, tare da ƙarfafa haɗin kai da mu’amala tsakanin Ghana da Zambia. TRT Hausa

 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#