Sport
Dollar
41,8580
0.03 %Euro
48,8948
0.23 %Gram Gold
5.707,4100
0.82 %Quarter Gold
9.796,4800
2.36 %Silver
71,2100
-0.32 %Gwamnan jihar Nasarawa ya ce kasancewar sabuwar ƙungiyar ta’addancin zai ta’azzara matsalar tsaro da dama ake fama da ita a yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce wani sabon reshe na ‘yan ta’addar Boko Haram da aka sani da suna ‘Wulowulo’ ya shiga yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Sule ya yi wannan bayanin ne ranar Litinin a wani taron masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.
Gwamnan ya ce kasancewar sabuwar ƙungiyar ta’addancin zai ta’azzara matsalar tsaro da dama ake fama da ita a yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya.
Ya ce akwai buƙatar a ɗauki matakan tsaro domin hana sabuwar ƙungiyar shiga jihar Nasarawa.
“Kamar yadda kuka sani, wannan sabuwar ƙungiyar mai suna Wulowulo, wadda wata ƙungiya ce wadda ta ɓalle daga Boko Haram, ta fara bayyana a arewa maso tsakiyar Nijeriya,” in ji Sule.
“A halin yanzu ƙungiyar Lakurawa wata babbar matsala ce a Kwara. Asali a da suna wuraren jihohin Kebbi da Sokoto ne, amma a halin yanzu sun yi ƙaurin suna a Kwara. Kwara ɗaya ce daga cikin jihohin arewa maso tsakiyar Nijeriya.
“Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa muka gayyace ku nan shi ne yanayin rashin tsaro, musamman a wasu sassan ƙasar nan, babban abin damuwa ne.
“Wasu daga cikinsu sun fara shiga jiharmu. Yana da mahimmanci mu ɗauki matakai domin tabbatar da cewa hakan bai faru ba.”
Gwamnan ya nuna damuwa game da yadda yawan garkuwa da mutane ke ƙaruwa a wasu sassan ƙananan hukumomin Lafia da Karu na jihar.
Ya ƙara da cewa akwai wata buƙata ta samar da sabuwar dabarar tsaro domin magance ƙaruwar yawan garkuwa da mutane da ake samu.
A ƙarshen shekarar da ta gataba, wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci, Lakurawa ta fara shiga wasu sassan jihohin Sokoto da Kebbi daga Jamhuriyar Nijar da Mali.
Comments
No comments Yet
Comment