Dollar

41,8527

0 %

Euro

48,9401

0.28 %

Gram Gold

5.662,7000

0.03 %

Quarter Gold

9.570,2800

0 %

Silver

70,7200

-1.01 %

Rahoton hukumar ya nuna saukar farashin abinci da kashi 2.34 cikin 100 a watan na Satumba, inda ya koma kashi 19.53 maimakon kashi 21.87 da yake a Agusta.

Hauhawar farashi a Nijeriya ta ragu da kashi 2.1 a watan Satumba - NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya, NBS ta ce hauhawar farashin kayayyaki ta ragu a ƙasar zuwa kashi 18 cikin 100 a watan Satumban da ya gabata.

A rahoton da hukumar ta saba fitarwa duk wata, ta ce an samu raguwar hauhawar farashin ne da kashi 2.1 a Satumba daga kashi 20.12 cikin 100 da yake a watan Agustan da ya wuce.

Rahoton hukumar ya nuna saukar farashin abinci da kashi 2.34 cikin 100 a watan na Satumba, inda ya koma kashi 19.53 maimakon kashi 21.87 da yake a Agusta.

Rahotanni suna cewa farashin kayayyakin abinci wanda su aka fi amfani da su a ƙasar na sauka, inda a watan Satumba aka samu ragi zuwa kashi 16.87 cikin 100 daga kashi 21,87 cikin 100 na watan Agusta.

NBS ta alaƙanta wannan raguwa da saukar farashin kayan abinci kamar masara da gero da garin kwaki da wake da dawa da dankali da albasa da ƙwai da tumatur da tattasai da sauran su.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#