Sport
Kwamitin Majalisar Shura na Jihar Kano ya ci gaba da aiki kan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar wa majalisar game da wa'azin sanannen malamin addinin Musuluncin, Sheikh Lawan Abubakar Shu'aibu, da aka fi sani da Lawan Triumph.
A Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, Majalisar Shura ta jihar ta yi wani zama na musamman da sanannen malamin addinin Musulunci da ke jihar, Sheikh Abubakar Shu’aibu Lawan
Malamin da aka fi sani da Lawan Triumph ya bayyana a gaban majalisar a wani zama da ya gudana a ofishin hedikwatar hukumar tsaro ta farin kaya, DSS reshen jihar Kano.
Zaman ya gudana ne ƙarƙashin Shugaban Majalisar Shurar, Wazirin Kano Malam Sa’ad Shehu Giɗaɗo, tare da taimakon sakataren majalisar da sauran ‘yan kwamitin binciken da aka kafa a baya.
Sauran mahalarta zaman sun haɗa da wakilan hukumomin tsaro a jihar, da manema labarai.
Tun makonni da suka wuce ne ƙungiyoyin addini a jihar suka gabatar da ƙorafe-ƙorafe a gaban majalisar kan wasu kalamai da mai wa'azin ya yi dangane da Annabi Muhammad (SAW).
Yadda zama ya kasance
Rahotanni sun ce, yayin zaman an kunna wa malamin wa’azozin da aka yi ƙorafi kansu har guda huɗu, inda ya tabbatar da cewa muryarsa ce, sannan aka gabatar masa da tambayoyi game da kalamansa cikin karatuttukan.
A jawabinsa, Sheikh Triumph ya ce, “Ƙofarmu a buɗe take musamman ni. Almajirinku ne ɗanku ne, a duk lokacin da aka ga abin da ba daidai ba wanda na yi, za a iya kira na.
“Wallahi ga duk waɗanda suka san ni, zan iya takowa in zo gidan kowane ne a cikin malamai a matsayin gidana ne, gidanmu ne, don in zo in ji nasiha kuma in ji faɗakarwa”, in ji malamin.
Daga bisani malamai daban-daban sun gabatar masa da nasiha da shawarwari, yayin da Sheikh Lawan Triumph ya gode wa kwamitin da gwamnatin Kano.
A ƙarshen zaman, kwamitin ya bayyana cewa zai miƙa rahoton zaman ga gwamnatin Kano domin ɗaukar mataki na gaba.
Comments
No comments Yet
Comment