Sport
Dollar
42,7285
0.01 %Euro
50,2071
-0.01 %Gram Gold
5.903,3200
0.02 %Quarter Gold
9.698,2800
0 %Silver
85,0400
0.12 %Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar rashin tsaftar muhalli da ƙarancin ruwa da cunkoso a wuri ɗaya su iya kaiwa ga ƙaruwar cututtukan numfashi masu tsanani, ciki har da mura, da kuma cututtukan hanta da na gudawa.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce aƙalla mutane 10 a Gaza sun mutu cikin sa'o'i 24 da suka gabata sakamakon ruwan sama mai ƙarfi, yayin da dubban iyalan Falasɗinawa masu gudun hijira ke ɓuya a tantuna ba tare da isasshiyar kariya daga mummunan yanayin hunturu ba.
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargaɗi a kafofin sada zumunta a ranar Asabar kan cewa akwai yiwuwar rashin tsaftar muhalli da ƙarancin ruwa da cunkoso a wuri ɗaya su iya kaiwa ga ƙaruwar cututtukan numfashi masu tsanani, ciki har da mura, da kuma cututtukan hanta da na gudawa.
Ya ce WHO na ci gaba da fuskantar matsaloli wajen isar da sinadaran ɗakin gwaje-gwaje da kayan gano cuta zuwa Gaza, inda ya lura cewa an hana shigar da yawancin kayayyaki bayan Isra'ila ta bayyana su a matsayin kayan amfani biyu.
Tedros ya yi kira da a gaggauta barin shigowar muhimman kayan, yana mai cewa suna da matuƙar muhimmanci wajen gano cututtuka, da kuma ba da magani cikin lokaci ga waɗanda ke fuskantar barkewar cuta a yankin.
Isra'ila ta kashe fiye da mutane 70,300, mafi yawan su mata da yara, kuma ta jikkata fiye da 171,000 a kisan ƙare-dangin da take yi a Gaza tun Oktoban 2023, wanda ya ci gaba duk da wata yarjejeniyar tsagaita wuta.
Sojin Isra'ila sun ta saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta, sun kashe aƙalla Falasɗinawa 386 kuma sun jikkata 1,018 tun lokacin da yarjejeniyar ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.
Comments
No comments Yet
Comment