Dollar

42,6137

0.03 %

Euro

50,1966

0.66 %

Gram Gold

5.843,6800

0.87 %

Quarter Gold

9.503,9100

-0.01 %

Silver

86,9600

2.76 %

Emine Erdogan ta yi kalaman ne a wani taron da ofishin watsa labaran Turkiyya ya shirya domin nuna bayanan Falasɗinawa mata da kuma fafatukar kafafen watsa labarai wajen ba da rahotanni daga Gaza.

Matar Shugaban Ƙasar Turkiyya ta karrama 'yanjarida Falasɗinawa

Matar Shugaban Ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta yi jinjina ga ‘yanjarida Falasɗinawa da aka kashe a Gaza, tana mai zargin Isra’ila da kai harin kan ma’aikatan kafafen watsa labarai da gangan tare da bayyana tunawa da su a matsayin “gwagwarmaya mafi ƙarfi”.

“Mun taru a nan a yau domin tunawa da kuma yin magana game da abin da muka shaida. Saboda tunawa ita ce gwagwarmaya mafi ƙarfi,” in ji Matar Erdogan a jawabinta da gabatar a wani taro na tunawa da ‘yanjaridar Falasɗinu wanda Hukumar Watsa Labaran Turkiyya ya shirya a ranar Talata a Ankara.

Taron ya haɗa ‘yanjarida da jami’ai da masu fafatuka domin nuna labaran da Falasɗinawa mata suka shaida da kuma fafatukar kafafen watsa labarai na bayar da rahoto daga zirin da aka yi wa ƙawanya.

Taron ya kuma samu halartar Shugaban Hukumar Watsa Labaran Turkiyya Burhanettin Duran, da Ministar Iyali da Tallafa wa Al’umma, Mahinur Ozdemir Goktas, da babban dakaratan TRT Mehmet Zahid Sobaci da shugaba kuma daraktan kamfanin dillancin labaran Anadolu Serdar Karagoz.

“Isra’ila ta kashe kusan ‘yanjarida 300 a cikin shekaru biyun da suka wuce. Talatin da bakwai daga cikinsu mata ne,” kamar yadda ta bayyana.

Erdogan ta buɗe jawabinta ne da jinjina ga ɗaya daga cikin matan, Selma Muheymer, tana mai siffanta ta a matsayin ‘yarjarida mai jarumta kuma uwa wadda ta yi shekarunta 31 a ƙarƙashin tashin bama-bamai da ƙawanyar Isra’ila.

‘Mamayar tana ci gaba’

Muheymer ta tafi Gaza a shekarar 2023 domin ganin iyalinta a karon farko cikin shekaru uku da kuma nuna musu jaririnta, Ali.

Jim kaɗan bayan ta isa, wani harin saman Isra’ila ya lalata gidansu, inda ya kashe ɗan mai shekara ɗaya da haihuwa tare da iyayen Muheymer da ‘yan’uwanta huɗu.

“A saƙo na ƙarshe da ta wallafa a shafinta na sada zumunta, Selma ta rubuta cewa: ‘Idan muka ɓace kuma ba a iya jin kowane labari daga gare mu ba, addu’a za ta haɗa mu,’” a cewar Erdogan.

Da take gabatar da jawabi a taron, Somaya M A Abunima ta TRT Arabi ta ce ta yi tafiya zuwa Gaza ranar 7 ga watan Oktoba, a shekarar 2023, inda ta bar ‘ya’yanta biyu a Istanbul, kuma ta shafe watanni biyu tana tattara bayanai game da lalace ababen. Ta bayyana fararen hula da ke rayuwa a ƙarƙashin hare-haren bama-bamai babu ƙaƙƙautawa, lamarin da ya ta’azzara yunwa da raba mutane da yawa da gidajensu, tana mai jaddada cewa “mamayar tana ci gaba.”

Da take Allaha wadai da abin da ta kira rashin adalci a martanain ƙasashen duniya, Abunima ta ce: “Duniya tana iya ƙoƙarinta a yau domin fitar da gawar wani ɗan-kama-wuri-zauna a Gaza, kuma ta yi shiru game da dubban ƙananan yara da iyalai da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai.”

Ta ƙara da cewa muryoyin Falasɗinawa na ci gaba da fitowa domin mata da ‘yanjarida da suka ci gaba da ba da rahoton abubuwan da ke faruwa daga wurin. “Idan har Falasɗinawa za su iya ci gaba da yin magana — ko ma daga ɗakunan da suka fi ƙanƙanta ne — gaskiya ba za ta mutu ba,” in ji ta.

Kafafen watsa labaran Ƙasashen Yamma da murɗa gaskiya

Ɗanjaraidan Falasɗinu, wanda mai fafatuka ne kuma mai haɗa fim da ya sami kyautar Oscar Basel Adra ya ce manema labarai da yawa ba su iya samun izinin shiga Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka yi wa ƙawanya ba, lamarin da ya hana su sanar da mutane yanayin da ake ciki a wurin.

Ya zargi Isra’ila da kama Falasɗinawa babu gaira babu dalili da kuma ƙin gurfanar da su a gaban kotu. “Yawancin waɗanda aka kama ‘yanjarida ne. ‘Laifinsu’ ɗaya kawai shi ne naɗar bidiyo, aikin jarida da kuma bayyana gaskiya,” in ji shi.

Adra ya kuma soki kafafan watsa labaran Ƙasashen Yamma da murɗe gaskiyar abin da ke faruwa a wurin.

“Kamar yadda na faɗa, yaƙi da gaskiya ya ɗaɗe da kasancewa manufar dakarun mamayar Isra’ila. Sai dai kuma, manyan kafafen watsa labarai a Ƙasashen Yamma suna yi wa wannan manufar hidima, inda suke ta murɗa gaskiya,” in ji shi.

Da yake ba da labarin abin da ya gani, Adra ya ce shi ya fara tattara bayanai game ababuwan da suka faru ne tun yana da shekaru kaɗan saboda fushi kan hare-hare da kame da kai samame gidaje.

“Na samu ƙrfin gwiwar ci gaba da naɗar bidiyo, domin ci gaba da bayyana gaskiya da kuma ci gaba da gabatar da labarina ga duniya,” in ji shi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#