Yara takwas na cikin waɗanda suka mutu a Kordofan ta Arewa

Harin jirgin RSF ya kashe ’yan gudun hijira 24 a Sudan

Wani hari da jirgin sama marar matuki da rundunar RSF ta kai kan wata mota da ke ɗauke da iyalai ’yan gudun hijira a tsakiyar Sudan ya kashe aƙalla mutane 24, ciki har da yara takwas, a ranar Asabar, kamar yadda Ƙungiyar Likitocin Sudan ta bayyana. TRT Hausa

Ƙungiyar ta ce harin ya afku ne kusa da birnin Rahad a lardin Kordofan ta Arewa, inda motar ke ɗauke da mutanen da suka tsere daga yankin Dubeiker sakamakon rikicin da ke ci gaba a yankin. TRT Hausa

Hukumar UNICEF ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce aƙalla yara 20 ne suka mutu a watan Janairu a Sudan, mafi yawansu a yankunan Kordofan da Darfur, tana mai gargaɗin cewa miliyoyin yara na buƙatar agajin gaggawa da kariya. TRT Hausa

Rikicin da ke tsakanin rundunar sojin Sudan da RSF tun daga Afrilun 2023 ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyin ’yan ƙasa da gidajensu, yayin da rikicin ke ci gaba da ta’azzara a sassa da dama na ƙasar. TRT Hausa

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#