An gina gidan ne ta gudunmawar jama’a a birnin Marka

’Yan Somali sun gina wa tsohon shugaban ƙasa Farmaajo gida

’Yan ƙasar Somalia sun gina wa tsohon shugaban ƙasa Mohamed Abdullahi Mohamed, wanda aka fi sani da Farmaajo, sabon gida a birnin Marka da ke bakin Tekun Indiya, ta hanyar tara gudunmawa daga jama’a a cikin gida da ƙasashen waje. TRT Hausa

An fara wannan yunƙuri ne a watan Yuni 2022, inda aka tara kimanin dala 300,000, sannan aka soma ginin a Yulin 2023, inda aka kashe kusan dala 295,000 kafin a buɗe gidan a hukumance ranar 6 ga Fabrairu. TRT Hausa

Tsohon shugaban ya nuna godiyarsa ga ’yan Somalia, fararen hula da jami’an tsaro da suka ba da gudunmawa, yana mai bayyana hakan a matsayin abin alfahari da haɗin kan al’umma. TRT Hausa

Masu bayar da gudunmawa sun yaba da salon shugabancin Farmaajo, suna cewa ya tafiyar da albarkatun ƙasa cikin hikima, ya inganta martabar Somalia a waje, kuma ya taimaka wajen rage wasu basussukan ƙasashen waje. TRT Hausa

Masana sun bayyana wannan mataki a matsayin wani muhimmin saƙo na shugabanci da girmamawa, wanda ka iya yin tasiri ba kawai a Somalia ba har ma a Afirka gaba ɗaya. TRT Hausa

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#