Dollar

40,5617

0.01 %

Euro

47,1994

-1.1 %

Gram Gold

4.317,9700

-0.79 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kwale-kwalen da ke 39 da buhuna ɗauke da fasinjoji 39 da buhunan shinkafa 50 daga ƙaramar hukumar Munya zuwa ƙaramar hukumar Shiroro ya kife ne a tsakiyar kogin Kwara.

Mutum 13 sun mutu, yayin da aka ceto 26 a hatsarin kwale-kwalen Jihar Neja ta Nijeriya - NEMA

Mutum 13 ne suka mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale ɗauke da matafiya 39 da ke kan hanyarsa ta zuwa ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja ta Nijeriya da safiyar ranar Asabar, a cewar wata sanarwa da hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa a Nijeriya, NEMA, ta fitar ranar Litinin.

NEMA ta ce mutanen da suka mutu sun haɗa da mata 8 da maza 3 da ƙananan yara 2.

Sanarwar ta ƙara da cewa an gano gawarwaki takwas daga cikin mamatan yayin da har yanzu ake neman saura mutane biyar.

Hatsarin ya auku ne yayin da kwale-kwalen ke tafiya da fasinjoji 39 da buhunan shinkafa 50  daga Shattai, Guni da ke ƙaramar hukumar Munya zuwa Kwatan, a kasuwar Zumba ta ƙaramar hukumar Shiroro, in ji sanarwar hukumar NEMA.

“An ceto matuƙin jirgin da sauran matafiya 25, inda ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira ke karɓan magani a asibitin gwamnatin jiha da ke Kuta,” in ji sanarwar.

Ofishin NEMA na Minna na sa ido kan lamurra tare da hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja da kuma hukumomi da ‘yan sa-kai domin tallafawa kan ayyukan ceton da ake yi,” in ji NEMA.

Batun hatsarin kwale-kwale dai a kogin Kwara da ke jihar Neja ya zama abin da ke faruwa kusan ko wace shekara a lokaci da damina ya yi nisa kuma yawan ruwan da ke cikin kogin ya ƙaru.

Ƙaruwar yawan ruwa cikin kogin yana sa masu tuƙa kwale-kwalen su kasa ganin kututture a cikin ruwa, lamarin da ke haddasa hatsari.

Kawo yanzu dai ba a bayyana abin da ya janyo wannan hatsarin ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#