Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Falasɗinawa mazauna Isra'ila sun yi watsi da batun, suna cewa abu ne da ke sake neman taɓa mutunci da asali da kuma tunzura mutane su yi ƙiyayya wa addini.
Ministan Tsaron Ƙasa mai ra'ayin riƙau na Isra'ila, Itamar Ben-Gvir, yana goyon bayan wani kudirin doka da zai hana kiran sallah a masallatai, yana ikirarin cewa hakan "yana damun" Yahudawa.
Kudirin doka da jam'iyyar Jewish Power ta Ben-Gvir ta gabatar zai hana kiran sallah sai dai idan masallatai sun sami amincewar gwamnati da kuma ɗaukar matakai kamar rage sauti da na ‘rage hayaniya’, da wurin da masallacin yake, da kuma kusancinsa da yankunan zama.
Falasɗinawa da ke Isra'ila sun yi suka ga matakin, suna cewa wannan mataki yana maimaita nufin kai hari kan asalinsu kuma yana ƙara tayar da husuma kan addininsu.
A ƙarƙashin wannan ƙuduri, za a bai wa 'yansanda izinin rufe lasifika nan take ko kum su ƙwace kayan.
Hukuncin tarar sun yi tsanani: idan aka sanya ko amfani da makirufo ba tare da izini ba za a ci tarar shekel 50,000 (US$15,660), yayin da za a ci tarar shekel 10,000 (US$3,100) idan aka keta sharuddan izini.
Wani irin shiri makamancin haka ya samu wucewa a majalisar dokokin Isra'ila (Knesset) a 2017 amma ba a taɓa aiwatar da shi ba.
Comments
No comments Yet
Comment