Dollar

42,2594

0.05 %

Euro

49,3682

0.75 %

Gram Gold

5.709,8500

0.21 %

Quarter Gold

9.714,9300

2.13 %

Silver

72,1500

-0.3 %

Ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na karya ƙa'idojin amfani da filaye ko kuma hana jami'an gwamnati gudanar da ayyukansu da ke kan ka’ida ba.

Ministan Abuja Nyesom Wike ya ce yana girmama sojoji

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike a ranar Alhamis, ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa yana amfani da batun mallakar filaye a Abuja don fada da sojojin Nijeriya, yana mai cewa koyaushe yana goyon bayan rundunar sojin.

Da yake magana da manema labarai kan rikicin da ya shafi jami'ansa da wasu jami'an soji, Wike ya bukaci 'yan Nijeriya da su koyi bin doka.

Ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na karya ƙa'idojin amfani da filaye ko kuma hana jami'an gwamnati gudanar da ayyukansu da ke kan ka’ida ba.

Ministan ya ce ayyukansa sun dogara ne kawai da doka, ba ra'ayi ko son-rai ba.

"Ana gaya maka ka bi umarnin da ke kan doka, ba umarnin da ba sa kan doka ba. Don haka, idan saboda kai jami’in tsaro ne, kana tunanin shugabanka ne ya umarce ka da ka harbi wani, kana ganin ba za a tuhume ka da laifin kisan kai ba ne saboda shugabanka ne ya ba ka umarnin?" ya tambaya.

"Mutane suna da matsaloli. Mun yi ƙoƙarin magance su, amma kada ka yi amfani da tsoratarwa, kada ka yi ƙoƙarin raunana gwamnati.

“Ba za ka iya raunana gwamnati ba. Domin idan muka yarda da wannan yanzu, wasu za su bi sahunka. Sannan za su ce, 'Lokacin da ya faru da wannan da wancan, me ka yi?'

“Jama’a, ni ina girmama sojoji. Zan ci gaba da girmama su. Don haka duk mai kokarin kawo gwara kawunanmu kan wancan batun, ‘ah, ai yana da matsala da sojoji ne,’ to ba haka ba ne. Ba ni da wata matsala da sojoji kuma ba zan samu wata matsala ba.”

"Idan muna da matsala da sojoji, na san inda zan je don kai korafi. Idan ban je wurin Babban Hafsan Tsaro ba, zan je wurin Babban Hafsan Sojoji, ko Babban Hafsan Sojan Ruwa, ko Sojojin Sama, ko Babban Jami'in Leken Asiri na Tsaro, zan je wurin Shugaban Kasa," in ji Wike.

Duk da haka Wike ya ce batun ya yi muni sosai ne saboda waɗanda suka dage suna nuna shi a matsayin wanda ke da rashin jituwa da sojoji.

Ya dage cewa ya shiga tsakani ne kawai bayan an ci zarafin manyan jami'an FCTA yayin da suke gudanar da ayyukansu na hukuma, yana mai cewa a matsayinsa na Minista, ba zai zauna a ofishinsa ba yayin da ake kai wa wadanda ke aiki tare da shi hari.

'Yan Nijeriya sun yi ta tofa albarkacin bakinsu sakamakon sa-in-sar da Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike ya yi da wani matashin soja mai suna A.M. Yerima a yayin duba wani fili da ya yi zargin cewa ba a bi doka wajen mallakarsa ba.

Taƙaddamar ta fara ne a lokacin da ministan ya yi tattaki da kansa zuwa filin mallakin wani tsohon babban hafsan sojin ruwa wanda aka jibge sojoji a cikinsa.

Wike ya nuna ɓacin ransa bayan sojan ya hana shi shiga filin, inda ya riƙa zagin sojan, matakin da wasu ke ganin bai dace ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#