Dollar

42,2448

0.05 %

Euro

48,9617

0.03 %

Gram Gold

5.625,5400

0.34 %

Quarter Gold

9.512,1700

-0.01 %

Silver

71,2000

2.36 %

Nijeriya da Amurka da Birtaniya suna aikin bincike a kan koken ɗin da kuɗinta ya kai dala miliyan 235 da aka kama a tashar jiragen ruwa ta Legas.

An kama hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1,000 a Nijeriya

Hukumar da ke yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta ce tana aiki da takwarorinta na Amurka da Birtaniya domin bincike kan asalin hodar ibilis da kimarta ta kai dala miliyan 235 da aka kama a tashar jiragen ruwa ta Tincan a Legas, ɗaya daga cikin kame mafi girma da aka yi a tarihin ƙasar.

Hukumar NDLEA ta bayyana a wata sanarwa ranar Talata cewa an gano kilogiram 1,000 na koken ɗin ne a cikin wata kwantena a wajen lodi da sauke kaya na tashar a ƙarshen mako.

Ma’aikatan tashar jiragen ruwan ne suka sanar da NDLEA da sauran jami’an tsaron tashar jiragen ruwan game da abin da ke faruwa.

Bayan an miƙa ƙwayoyin ga hukumar NDLEA ranar Talata, gwaje-gwaje sun tabbatar da cewa hodar koken ce.

Hukumomin da ke yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi na Amurka da na Birtaniya sun shiga cikin masu binciken bisa gayyatar gwamnatin Nijeriya.

"Maƙasudin haɗin kai da abokan aikinmu na ƙasa da ƙasa  shi ne tabbatar da cewa ba a bar wata dama ba... saboda mu iya kama da kuma hukunta duk waɗanda suka kitsa aika wannan a duk inda suke a duniya," kamar yadda Reuters ta ambato shugaban NDLEA, Buba Marwa, yana cewa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#