Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Da yake tabbatar da lamarin kyaftin ɗin Super Eagles, Willam Troost-Ekong, ya ce da zarar an warware matsalar, su da kansu za su sanar da hakan.

‘Yan wasan Super Eagles sun ƙaurace wa atisaye kan rashin biyansu alawus

‘Yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles, sun ƙaurace wa atisayen shirin wasannin shiga gasar cin kofin duniya kan rashin biyansu alawus.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, wani ɗan jarida da yake aiki kan harkar wasanni a Nijeriya, Oluwashina Okeleji, ya ce ‘yan wasa da jami’an tawagar ta Super Eagles sun ƙaurace wa atisayen ne saboda batutuwa na alawus alawus da ba biya su ba.  

“[Suna] jiran warware matsalar da wuri domin su ci gaba da shirya wa wasan ranar Alhamis,” in ji Okeleji.

Da yake tabbatar da lamarin kyaftin ɗin Super Eagles, Willam Troost-Ekong, ya ce da zarar an warware matsalar, su da kansu za su fara bayyana hakan.

“Duk wata sanarwa ko iƙirari  ko kuma wata buƙata bayan buƙata [ta alawus] ta gaskiya da aka yi rubutu a kai ba gaskiya ba ce,” in Troost-Ekong, yana mai ishara ga saƙon da Okeleji ya wallafa.

“Abin da muke so kuma muke ci gaba da yi shi ne mu mayar da hankali kan muhimman wasannin da ke gabanmu,” in ji shi.

Nijeriya dai za ta kara da Gabon a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya.

Gurbi ɗaya tilo ne ya yi saura da wata ƙasar Afirka za ta iya cikewa a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 kuma ƙasashen Nijeriya da Gabon da Kamaru da kuma Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ne ke neman samun damar.

Nijeriya za ta kara da Gabon ranar Alhamis da misalin ƙarfe biyar agogon Nijeriya yayin da Kamaru za ta kara da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da misalin ƙarfe takwas agogon Nijeriya.

Ƙasashen da suka yi nasara a wasannin kuma za su kara a ƙarshen mako inda za a samu ƙasar da za ta wakilci Afirka a zagaye na ƙarshe na neman shiga gasar cin kofin duniya.

Za a yi wasannin ranar Alhamis da ƙarshen makon ne a ƙasar Maroko, kuma tuni yawancin ‘yan wasan da kocin Nijeriya ya gayyata suka isa ƙasar da ke arewacin Afirka.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#