Sport
Dollar
41,8395
0.03 %Euro
48,7779
0.37 %Gram Gold
5.661,3600
1.66 %Quarter Gold
9.570,2800
2.24 %Silver
71,4800
3.26 %Bayan tsagaita wuta mai rauni tsakanin Isra'ila da Hamas, shirin zaman lafiya mai matakai da dama na nufin kawo ƙarshen yaƙin da kuma sake gina Gaza, idan har za a iya shawo kan manyan kalubale.
Bayan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, hankula yanzu sun karkata kan mataki na gaba na wani shirin zaman lafiya mai cike da buri, wanda aka tsara domin kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila mai tsanani a Gaza da kuma kafa harsashin zaman lafiya mai ɗorewa.
An dakatar da hare-haren bama-bamai kuma sojojin Isra'ila sun janye daga Gaza a ranar Jumma’a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma tsakanin Isra'ila da Hamas.
A halin yanzu, kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta saki dukkan Isra'ilawa 20 da take tsare da su a matsayin musayar fursunonin Falasdinawa, kuma an fara samun ƙarin agaji da ke shiga yankin Falasdinawa bayan shekaru biyu na mummunan yaƙi.
Ƙasashen Masar da Qatar da Turkiyya sun rattaba hannu tare da Shugaban Amurka Donald Trump kan wata takarda game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza a ranar Litinin, yayin wani taron ƙasa da ƙasa da Masar ta shirya a birnin shaƙatawa da ke gaɓar Bahar Maliya, wato Sharm el-Sheikh.
Shirin zaman lafiyar yana da matakai da dama, kowanne yana da manyan ƙalubale da za a fuskanta.
Mene ne matakai uku na shirin?
Mataki na farko, wanda aka riga aka fara, ya haɗa da tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu da sakin fursunoni daga ɓangarorin biyu, da kuma ƙara samun damar shigar da kayayyakin agaji ga yankin Falasɗinawa.
Masu shiga tsakani na ƙasa da ƙasa sun ce wannan matakin yana aiki amma yana da rauni, saboda rashin amincewa tsakanin ɓangarorin.
Mataki na biyu, wanda ake ganin shi ne mafi wahala, zai mayar da hankali kan rushe tsarin sojin Hamas, ciki har da makamai da rumbunan roka da kuma hanyoyin ƙarƙashin ƙasa.
Ana iya bai wa mayakan Hamas afuwa ko damar fita ƙasashen waje idan sun ajiye makamai.
Domin kauce wa giɓin iko, za a tura wata rundunar kiyaye zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa, mai yiwuwa ta haɗa da sojojin ƙasashen Larabawa da abokan ƙawancen NATO, domin tabbatar da tsaro a wurare masu mahimmanci da kuma kula da sauyin iko.
Sojojin Isra'ila za su fara janyewa a hankali yayin da rundunar ƙasa da ƙasa za ta karɓi iko.
Isra'ila tana son tabbatar da cewa Hamas ta ajiye makamai, yayin da Hamas ke son tabbatar da cewa Isra'ila ta janye duka daga Gaza ba tare da sake farfaɗo da yaƙin ba.
Amma har yanzu ba a san tsawon lokacin da wannan zai ɗauka ba—makonni, watanni, ko shekaru.
Shirin maki 20 da Trump ya gabatar ya bukaci Isra'ila ta ci gaba da rike wani yanki mai kunkuntar tsaro a cikin Gaza kusa da iyakar su, tare da rike yankin Philadelphi Corridor, wani yanki a kan iyakar Gaza da Masar.
Isra'ila ba za ta yarda ta mika wadannan yankuna ba sai Hamas ta ajiye makamai.
A lokaci guda, dole ne a tsara wata sabuwar gwamnati a Gaza domin maye gurbin mulkin Hamas.
Ba tare da wannan ba, ba za a iya fara sake gina Gaza ba, wanda zai bar mutane fiye da miliyan biyu cikin halin kunci.
Tare da rashin amincewa tsakanin bangarorin, yawancin abin ya dogara ne kan ci gaba da matsin lamba daga masu tabbatar da yarjejeniyar.
Duk wata matsala wajen warware wadannan batutuwa masu sarkakiya na iya lalata komai kuma ta haifar da Isra'ila ta sake farfado da yakin ta na lalata Gaza.
Shirin Trump mai matakai 20 ya kuma bukaci wata rundunar tsaro ta ƙasa da ƙasa da Larabawa za su jagoranta ta shiga Gaza, tare da 'yan sanda Falasdinawa da aka horar a Masar da Jordan.
Ya ce sojojin Isra'ila za su bar yankunan yayin da waɗannan rundunoni za su mamaye.
Idan an samu nasarar kawar da makamai, za a mayar da hankali kan sake gina gine-ginen Gaza da aka lalata a ƙarƙashin mataki na uku.
Ana sa ran za a samu biliyoyin tallafi daga masu bayar da gudunmawa na ƙasa da ƙasa, ciki har da EU, da ƙasashen Gulf, da Amurka.
Za a kafa wata gwamnatin riƙon ƙwarya mai zaman kanta domin kula da sake gina Gaza, wanda zai share fagen miƙa mulki ga Hukumar Falasdinawa ko wata sabuwar hukuma da za ta wakilci Gaza da Yammacin Kogin Jordan.
Me manyan masu ruwa da tsaki ke cewa?
Manyan shugabannin duniya sun bayyana ra'ayoyinsu kan tsagaita wutar da kuma matakan shirin zaman lafiya.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce aikin wahala ya fara yanzu yayin da mataki na farko na tsagaita wuta ya fara aiki.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da ƙudurin kare tsaro, amma ya nace cewa dole ne a ƙwace makaman Hamas domin zaman lafiya ya ɗore.
Hamas ta amince da tsagaita wutar amma ta yi kira da a ci gaba da kula da hakkokin Falasdinawa.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce zaman lafiya mai ɗorewa a Gaza zai yiwu ne kawai da mafita ta kasashe biyu.
Ya jaddada bukatar ci gaba da kai agaji ba tare da katsewa ba zuwa Gaza da kuma fara sake gina ta ba tare da ɓata lokaci ba.
A yayin taron a Sharm el-Sheikh kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas da makomar Gaza, Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi ya shaida wa shugabannin duniya a ranar Litinin cewa shirin Trump shi ne "damar ƙarshe" don samun zaman lafiya a yankin.
A halin da ake ciki, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, ya kuma yi kira da a ba da damar kai agaji ba tare da wani cikas ba kuma ya jaddada cewa "dole ne a dakatar da yaƙin gaba daya," tare da danganta tsagaita wutar da sake farfado da wani tsarin siyasa mai inganci na mafita ta samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu.
Makomar Gwamnati
Duk da cewa shirin zaman lafiya na yanzu ya fi mayar da hankali kan tsagaita wuta da kuma tabbatar da kwanciyar hankali, ya kauce wa batutuwan asali na samun 'yancin Falasdinawa da tattaunawar matsayi na ƙarshe.
Masana da dama suna ganin wannan tsarin mataki-mataki a matsayin matakin farko mai mahimmanci don farfado da tattaunawar mafita ta samar da ƙasashe biyu da aka daɗe ana dakon ta.
Duk da haka, har yanzu akwai rashin tabbas kan yadda da kuma lokacin da za a iya samun cikakkiyar ƙasar Falasdinawa mai cin gashin kanta, la'akari da rabuwar siyasa da kuma rikice-rikicen yankin.
Masu suka suna gargadi cewa ƙwace makaman Hamas na iya zama abin da ba zai yiwu ba, kuma akwai damuwa kan ko mutanen Gaza za su amince da wata hukuma da aka ƙaƙaba daga waje.
Haka kuma, batutuwan kudi da hadin kai suna nan a matsayin manyan ƙalubale, tare da barazanar sake ɓarkewar rikici.
Duk da waɗannan rashin tabbas, masu ruwa da tsaki na ƙasa da ƙasa suna ganin wannan tsarin mataki-mataki a matsayin mafi kyawun damar da aka samu cikin shekaru don tabbatar da zaman lafiya a Gaza da kawo ƙarshen jerin yaƙin da bala'in jinƙai.




Comments
No comments Yet
Comment