Dollar

41,3038

0.05 %

Euro

48,8264

0.03 %

Gram Gold

4.839,7500

-0.36 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An bai wa baƙi waɗanda suka halarci bikin damar fahimtar yadda tsarin tsaron sararin samaniya na Steel Dome ke aiki domin kawar da duk wata barazanar hari ta sama.

Maziyarta Teknofest sun samu damar fahimtar yadda fasahar Steel Dome ta Turkiyya ke aiki

Kamfanin Tsaron Turkiyya na ASELSAN, ya kafa wata rumfa a filin da ake gudanar da bikin Teknofest a Istanbul inda yake bayar da dama baƙi su fahimci yadda tsarin tsaron sararin samaniya na Steel Dome ke aiki domin kawar da duk wata barazanar hari ta sama.

An fara wannan babban taron fasaha da jiragen sama na kwanaki biyar na Teknofest a Istanbul a ranar Laraba.

An shirya wannan biki ne ta hanyar haɗin gwiwar Asusun Turkish Technology Team (T3) da Ma’aikatar Masana’antu da Fasaha ta Turkiyya.

A cikin wannan biki, ana gudanar da abubuwa daban-daban, daga gasar fasaha zuwa zuwa baje-kolin jiragen sama da marasa matuƙa da kuma wasan jiragen.

An kuma yi baje-kolin sassa daban-daban na tsarin Steel Dome a wurin bikin domin masu kallo,

Ta hanyar amfani da na’ura ta zamani ta hoto, masu ziyarar na iya ganin yadda Steel Dome ɗin ke bayar da kariya ko da an samu wata barazana.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#