Dollar

40,2605

0.14 %

Euro

46,8089

0.25 %

Gram Gold

4.325,1100

0.65 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Bayan daukar lokaci mai tsayi a yanayin sanyi, dusar kankara ta barbade birnin Istanbul inda jama’a ke murna da yadda ka’ina ya yi fari fat.

Mazauna Istanbul sun marabci dusar ƙanƙarar da aka jima ana jira inda birnin ya yi fari fat

Daga Karya Naz Balkiz

‘Yan shekarun da suka wuce ba a samu zubar kankkara a Istanbul ba. Baya ga rashin zubar kankarar, ga dimbin cunkoson ababen hawa da sauyin yanayi da ya damu birnin, amma a ranar Larabar nan lamarin ya sauya.

Iyaye dama irin su Gul Ece Cakmak sun ji dadin zubar dusar ka kankarar, inda mahaifiyar yara biyu ta yi gaggawar zuwa dauko ‘yarta daga makarantar reno don ta yi wasa a dusar kankara.

“Suna shewar farin ciki a lokacin da suke tafiya gida, suna kallon dusar kankarar na zuba a jikin takar mitarsu,” in ji ta.

A wajen ‘yarta Duru mai shekaru 6, hada mutum-mutumi da dusar kankarar shi ne cinyewa a lokacin sanyi.

“Idan kankarar ta taba fuskata akwai sanyi. Amma na hada mutum-mutumi da ita, ba na jin sanyin sosai,” ta fada aa TRT Afrika.

A wajen Bade mai shekaru biyu kuma, wannan dusar kankarar lamarinne mai girma a rayiwarta saboda ita ce ta farko da ta gani.

"Dusar kankarar da ta zuba a makin da ya gabata ba ta da yawa, shi ya sa ba mu wani gahimci bambanci ba.

"Amma a wannan karon, na ji dadin ganin dan hancinta ya yi ja saboda daga kanta sama tana kallon yadda fale-falen dusar kankara ke zuba a kan fuskarta,” Cakmak ta fadi haka game da Bade.

Duk da Bade ba za ta iya bayyana me take ji ba, kawai tana ta maimaita kalma daya ne “Kar” dusar kankara kenan a harshen Turkanci.

An soke tashi da saukar jiragen sama, an dakatar da zirga-zirgar ababen hawa

A yayin da yara ke murna da farin ciki kan “hutun makaranta saboda dusar kankara”, an samu tsananin cunkoson ababan hawa a Istanbul a yammacin Laraba. Inda matafiya sula dauki awanni kafin su je inda suke son zuwa.

A yayin da aka rufe hanyoyi tare da jinkirta mitsawar motocin bas, mutane sun yi dogayen layuka suna jiran zuwan motocin, wasu kuma sun taka da kafa zuwa gida.

Haka kuma, manyan filayen jiragen saman Istanbul guda biyu sun rahe yawan jiragen da za su kula da su. Kamfanin jiragen saman Turkiyya, ya kansile tashi ln jiragen sama 200.

A yayin da dusar kankarar ta dinga sauka a mashigar tekun Istanbul, Ma’aikatar Sufuri da Gina Kasa ta sanar da dakatar da kai komon jiragen ruwa a mashigar.

Fatma Korunoglu, wata mazauniyar Istanbul ta ce dusar kankarar ta yi yawa ta yadda ba ta iya ganin gasar shahidai ta Istanbul.

A wajenta, saukar dusar kankarar ya zo da makararren farin ciki saboda yasda aka dade ba a ga hakan ba. Ta ce dusar kankarar ta karfafa gwiwar mutane, inda ta sanya su mantawa da matsalolinsu na yau.

“A yayin tafiya a Istanbul, na gani wani abu… alamun farin ciki a fuskokin mutane, har ma a ababan hawa na haya,” ta fada wa TRT World, tan amai kara wa da cewa wasu iyalan m tuni suka fita waje don tattara dusar kankarar ta yammacin Laraba.

Hukumar Kula da Yanayi ta ce dusar kankarar za ta ci gaba a ranar Alhamis a fadin Istanbul har zuwa ranar Litinin din mako mai zuwa.

A wurare masu tsananin tudu ma za ta iya kai santimita 40. / Hoto: AA

Gwamnan Istanbul, Davut Gul ya bukaci mazauna birnin da su kaurace wa tafiyar da ba ta dole ba, su hakura da amfani da ababan hawanau ba tare da tayoyin lokacin sanyi ba, kuma su dogara kan ababan hawa na haya masu daukar mutane da yawa.

Ana sa ran yankunan da ke gabar teku za su samu zubar dusar kankara har ta kai tudun santimita 5 zuwa 10, inda yankunan da babu teku kuma za su fuskanci mai yawan santimita 20 zuwa 20 ko ma sama da haka a ranakun Juma’a da Asabar.

A wurare masu tsananin tudu ma za ta iya kai santimita 40.

Ana sa ran yanayi zai sauka zuwa daraja 0 zuwa 2 har nan da 22 ga Fabrairu, kai har za a iya samun saukarta zuwa -1 ko -2, in ji masanan yanayi.

Dusar kankarar na kuma sauka a yankin Tekun Bahar Maliya, inda ake sa ran sanyi zai yi yawa a garuruwa da dama. Babban birnin Ankara da aasu garuruqa sa dama na tsakiyar Anatolia na fuskantar sanyi da kankarar.

Lokutan sanyi da ba a saba gani ba

Lokutan da aka fi samun zubar dusar kankara sosai a Istanbul su ne 1987, 2004, 2017, da 2022.

Korunoglu da ta zo daga garin Mersin na yankin Tekin Bahar Rum da ba a samun zubar dusar kankara sosai, ta ji dadin yadda yanayin sanyi ya kasance a Istanbul.

“A Mersin, iyaye na kai yaransu Taaunukan Taurus don su ga dusar kankara,” in ji ta. A zaman da ta yi a Istanbul, ta fahimci yadda dusar kankara ke hada mutane waje guda suna wasanni tare.

“Idan dusar nanzuba, kowa na son fita waje, komai irin sanyin da ake yi. Ko karfe 1 na dare ne, za ka ga mutane a waje, na jin dadin zubar ta.”

A ranakun da dusar kankara ke zuba, tana tabbatar da ta tsaya a mashigar tekun Istanbul din shaida yadda ‘yan Istanbul suke.

“Tekun na sauya kala zuwa kore shar tare da rangaji idan dusar kankara na zuba.”

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#