Sport
Dollar
41,1468
0.24 %Euro
48,1459
0.08 %Gram Gold
4.564,0100
1.21 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Romelu Lukaku na Napoli ya samu rauni a cinya yayin wasan sada-zumunta na share fagen gasar Serie A ta Italiya.
Ɗan wasan Napoli, Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa yayin wasan sada-zumunta da Olympiacos, kafin fara gasar Serie A ta Italiya.
Raunin zai tilasta masa tafiya jinyar watanni uku har zuwa Nuwamba, kamar yadda Napoli ta tabbatar a wata sanarwa.
Sanarwar ta ce, "Sakamakon raunin da ya samu yayin wasa da Olympiacos, an yi wa Romelu Lukaku gwaje-gwaje a asibitin Pineta Grande Hospital, wanda ya bayyana babban rauni a ƙashin cinyarsa ta hagu. Ɗan wasan tuni ya fara samun kulawa kuma zai samu shawar likita kan tiyata."
An yi wa ɗan wasan ɗan asalin Belgium gwajin likita a asibitin Pineta Grande Hospital, kuma rahotanni sun nuna ya samu babban rauni a ƙashin cinyarsa.
Lukaku dai yana da babban tasiri a ƙungiyar Napoli a baya-bayan nan ƙarƙashin koci Antonio Conte, wanda a baya sun yi aiki tare a Inter.
Comments
No comments Yet
Comment