Yaƙin Isra'ila a Gaza yana kwana na 381, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,603 da raunata kusan 100,000, inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,464 a Lebanon tun Oktoban bara.

Kai-tsaye: Karin sojojin Isra'ila 23 sun jikkata yayin da rikici ya tsananta a Gaza da Lebanon

Litinin, 1 ga watan Oktoban 2024

1406 GMT — Lebanon ta ce harin da Isra'ila ta kai a babban birnin Baalbek da ke gabashin kasar ya kashe mutum shida ciki har da wani yaro, yayin da kafafen yada labarai na kasar suka rawaito cewa harin ya afka wa wani gini da ke wani yanki mai cike da cunkoso.

"Harin da makiyanmu Isra'ila suka kai...a Baalbek ya kashe mutane shida, ciki har da wani yaro," in ji ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon, kuma kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito cewa dukkan mutanen shida 'yan gida daya ne.

1427 GMT — 23 more Israeli soldiers injured as clashes intensify in Gaza, Lebanon

At least 23 more Israeli soldiers were injured in clashes in Gaza and southern Lebanon in the last 24 hours, the military said.

Israeli military figures showed that six of the soldiers were wounded in Gaza, without specifying where the rest of the soldiers were injured.

According to the figures, at least 749 soldiers have been killed and 5,018 others injured since the outbreak of the Gaza conflict on October 7, 2023.

1427 GMT — Karin sojojin Isra'ila 23 sun jikkata yayin da rikici ya tsananta a Gaza da Lebanon

Aƙalla ƙarin sojojin Isra'ila 23 sun sami raunuka a arangamar da aka yi a Gaza da kuma kudancin Lebanon cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Alkaluman sojin Isra'ila sun nuna cewa shida daga cikin sojojin sun jikkata a Gaza, ba tare da bayyana inda sauran sojojin suka jikkata ba.

Alkaluman sun ce akalla sojoji 749 ne aka kashe yayin da wasu 5,018 suka jikkata tun bayan barkewar rikicin Gaza a ranar 7 ga Oktoban 2023.

#