Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 420 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,330 da jikkata fiye da mutum 104,933. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktobar bara.
0435 GMT — Sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla takwas, daga ciki har da biyar waɗanda 'yan gida ɗaya ne a wasu jerin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a faɗin Gaza.
A wani hari da aka kai a sansanin gudun hijira na Nuseirat, mutum biyar ne suka rasa rayukansu.
Hukumomin Isra'ila sun bayar da rahoton cewa akwai wasu mutum uku da suka rasu a wani hari na daban da Isra'ilar ta kai yammacin birnin Gaza.