Sport
Dollar
38,5780
0.01 %Euro
43,6938
0.06 %Gram Gold
4.105,5600
2.16 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Kafar watsa labaran Isra'ila ta Channel 12 ta ce, a ƙarƙashin shirin kuma akwai niyyar mayar da Falasdinawa kudancin Gaza daga arewa.
Ministocin Isra'ila sun amince da wani shiri na mamaye dukkan yankin Gaza da kuma kasancewa a wurin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito wasu jami'ai biyu suna cewa.
Wannan ya biyo bayan amincewar Majalisar Tsaron Isra'ila a ranar Litinin da shirin faɗaɗa hare-haren soji da suke yi a Gaza tare da mamaye wasu yankuna a cikin wannan gunduma.
A cikin wata sanarwa, ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Majalisar Ministocin ta amince da "shirin aiki" da shugaban sojoji Eyal Zamir ya gabatar domin "murkushe Hamas" da kuma dawo da mutanen Isra'ila da ake tsare da su a Gaza.
Sanarwar ta ƙara da cewa, shirin ya bukaci sojojin su "mamaye Gaza da kuma riƙe yankin a ƙarƙashin ikonsu."
Gidan talabijin na Isra'ila Channel 12 ya bayyana cewa shirin ya kuma haɗa da korar Falasdinawa daga arewacin Gaza zuwa kudancin yankin.
Babu wani martani nan take daga bangaren Falasdinawa kan wannan shirin na Isra'ila.
Sojojin Isra'ila sun riga sun fara aika dubban takardun kiraye-kiraye ga sojojin ko-ta-kwana domin ƙara yawan dakarun da za su shiga wannan farmaki a Gaza, kamar yadda shugaban sojoji Laftanar Janar Eyal Zamir ya bayyana a wata sanarwa a ranar Lahadi.
Isra'ila ta sake dawo da hare-harenta a Gaza a watan Maris bayan ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta tallafa, wadda ta dakatar da fada na tsawon watanni biyu.
Comments
No comments Yet
Comment