Sport
Dollar
38,5992
0.33 %Euro
43,6545
0.2 %Gram Gold
4.017,2800
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Rahotanni sun ce da safiyar Asabar, sojojin saman Isra’ila sun kai hare-haren ne a wajen birnin Harasta da ke kusa da Damascus inda sauran hare-haren kuma suka faɗa wasu wurare biyu da ke yammacin yankunan Hama da Latakia.
Isra'ila ta kai hari a kusa da birnin Damascus na kasar Syria da kuma lardunan Latakia da Hama, bayan da Isra'ila ta kai hari kusa da fadar shugaban kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Syria SANA ya ruwaito.
Rahotannin sun ce da safiyar Asabar, sojojin saman Isra’ila sun kai hare-haren ne a wajen birnin Harasta da ke kusa da Damascus” inda sauran hare-haren kuma suka faɗa wasu wurare biyu da ke yammacin yankunan Hama da Latakia.
Rahotanni sun ce an jikkata mutum huɗu a Hama.
Da sanyin safiyar Juma'a ne Isra'ila ta kai harin bam a wani yanki da ke kusa da fadar shugaban kasa a Damascus.
Fadar shugaban ƙasar Syria ta yi Allah wadai da harin da Isra'ilar ta kai ta sama, tana mai cewa "hatsari ne wanda zai iya rura wutar rikici ga ƙasar da kuma ikon ƙasar.”
Fadar shugaban Syriar ta kuma yi kira ga ƙasashen duniya da su goyi bayan Syria, tana mai cewa irin waɗannan hare-haren suna shafar tsaron ƙasar Syria ne da hadin kan al'ummar Syria.
Comments
No comments Yet
Comment