Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 204 tana yi a Gaza ya kashe 34,388 Falasɗinawa — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — sannan mutum sama da 77,437 sun jikkata, yayin da ake fargabar mutum 8,400 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.
1135 GMT –– Isra'ila ta kashe ƙananan yara 8 a sabbin hare-haren da ta kai Gaza
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa sama da goma sha biyu, ciki har da ƙananan yara takwas a harin bam da ta kai Gaza ranar Asabar, a cewar kafar watsa labaran Falasɗinu.
Ta kai harin ne a wani gida da ke yankin Saudi na birnin Rafah. Falasɗinawa aƙalla shida, ciki har da ƙananan yara huɗu ne suka mutu a wannan harin, in ji kamfanin labarai na Wafa. Kazalika mutum aƙalla takwas sun jikkata.
Haka kuma jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a yankin Jaradat da ke gabashin Rafah, inda suka jikkata mutane da dama, kamar yadda ganau suka tabbatar wa da kamfanin labarai na Anadolu.
A Gaza, harin da Isra'ila ta kai ta sama a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa tara, cikinsu har da ƙananan yara huɗu, tare da jikkata mutum 30, a cewar majiyoyi daga asibitin yankin.
Wani wakilin Anadolu ya ce ma'aikatan ceto sun zaƙulo gawawwaki huɗu da kuma mutane da dama da suka jikkata a ƙarƙashin ɓaraguzan wani gini awanni bayan Isra'ila ta kai masa hari ta sama.
Sannan jiragen yaƙin Isra'ila sun yi ɓarin wuta a sansanonin Nuseirat da Bureij kana suka rusa wasu gidaje a garin Al-Mughraqa na tsakiyar Gaza, in ji shi.
0914 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya kai 34,388
Ma'aikatar kiwon lafiya ta Falasɗinu ta ce kawo yanzu adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a yankin ya kai 34,388.
Mutanen da suka mutu sun haɗa da mutum 32 da dakarun Isra'ila suka kashe a awanni 24 da suka gabata, a cewar ma'aikatar kiwon lafiyar.
Ta ƙara da cewa mutane 77,437 sun jikkata a Gaza tun da Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a yankin ranar 7 ga watan Oktoba.
0906 GMT — Mutum ɗaya ya mutu yayin da Isra'ila ta yi luguden wuta a wasu garuruwa na kudancin Lebanon
Aƙalla mutum guda ya mutu a Lebanon yayin da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai hare-hare biyu a garuruwan Kafr Shuba da Shebaa da ke kudancin ƙasar.
"Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai samame sau biyu da sanyin safiya a garuruwan Kafr Shuba da Shebaa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Qasim Asaad a garin Kafr Shuba da kuma rusa gidaje biyus," a cewar kamfanin dillancin labarai na Lebanon.
Kawo yanzu Isra'ila ba ta ce komai game da wannan batu ba.
0043 GMT — Hamas ta ce tana nazari kan sabbin sharuɗɗan tsagaita wuta na Isrra'ila
Ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta ce ta karbi bayanai daga Isra'ila game da sabbin sharuddan tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su kuma tana yin nazari a kansu.
"A yau, ƙungiyar Hamas ta karɓi bayabai daga Yahudawa ƴan mamaya game da batun tsagaita, waɗanda masu shiga tsakanin daga Masar da Qatar suka gabatarranar 13 ga watan Afrilu," a cewar Khalil al Hayya, mataimakin shugaban ɓangaren siyasa na Hamas, a wata taƙaitacciyar sanarwa da ya fitar.
"Ƙungiyarmu za ta yi nazari a kansu, kuma da zarar mun kammala za mu bayar da amsa."

