Sport
Dollar
43,4908
0.04 %Euro
51,4421
0.27 %Gram Gold
6.847,4000
5.29 %Quarter Gold
11.661,9400
0 %Silver
120,6200
7.89 %An kai harin ne a Tyre duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Nuwamban 2024
Isra’ila ta kashe mutum guda tare da jikkata wasu biyu a wani hari ta sama da ta kai a kudancin Lebanon, abin da aka bayyana a matsayin karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma tun watan Nuwamban 2024. Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta ce an kai harin ne ranar Litinin a garin Tyre, inda Cibiyar Ayyukan Lafiya na Gaggawa ta tabbatar da asarar rai da jikkatawar. TRT Hausa
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa na Lebanon (NNA) ya rawaito cewa wani jirgi marar matuki na Isra’ila ne ya doki wata mota a wajen Tyre. Rahoton ya kara da cewa wasu jiragen Isra’ila na shawagi a sararin samaniyar yankuna da dama a kudancin kasar, inda aka jefa bam mai kara a kan wani kamfanin marble da ke kan hanyar Adissa–Markaba. TRT Hausa
Kungiyar Hezbollah ta sanar da cewa harin da aka kai a Tyre ya yi sanadin mutuwar dan jaridar gidan talabijin na Al Manar, Ali Nour Al Din, bayan da aka kai hari motarsa. Kungiyar ta yi Allah-wadai da kisan, tana mai gargadin hadarin kai hare-hare kan fararen hula da ma’aikatan kafafen watsa labarai. TRT Hausa
A wani rahoto na daban, NNA ya ce wata tankar Isra’ila ta kai hari kan wani gida a wajen garin Aitaroun da ke gundumar Bint Jbeil, yayin da aka kuma kai hare-haren bama-bamai a yankin Hreika daga wani sabon sansanin soji da Isra’ila ta kama. Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a kudancin Lebanon duk da yarjejeniyar tsagaita wuta. TRT Hausa
Comments
No comments Yet
Comment