Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Gwarzon ɗanwasan boksin, Anthony Joshua ya samu hatsarin mota a jihar Ogun ta Nijeriya, inda rahotanni suka ce har mutum biyu sun rasa ransu a motar da yake.
Rahotanni daga Nijeriya na cewa hatsarin mota ya rutsa da gwarzon ɗan damben boksin na Burtaniya ɗan asalin Nijeriya, Anthony Joshua.
Hatsarin wanda hukumomi suka tabbatar ya afku ne a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Nijeriya, kuma ya bar Joshua da raunuka ba masu tsanani ba.
Mai shekaru 36, Joshua yana tafiya ne cikin mota ƙirar Lexus jeep kan hanyar Lagos zuwa Ibadan, inda motar ta yi karo da wata babbar mota da aka ajiye a gefen hanya.
Joshua yana da dangi a garin Sagamu na jihar Ogun ya tabbatarwa majoyoyin ‘yansanda cewa yana cikin ƙoshin lafiya, duk da rahotanni sun ce mutane biyu sun halaka sakamakon hatsarin.
A halin yanzu wasu hotuna na ta yawo a kafofin yaɗa labarai wanda ke iƙirarin nuna abin da ya faru bayan hatsarin, inda aka ga mota da gilashi a fashe.
Jaridar Punch ta Nijeriya ta nuna wani hoton Anthony Joshua yana zaune a kujerar bayan motar da ta lalace daga gabanta.
Ɗanwasan dai ya kai ziyara Nijeriya ne domin hutun ƙarshen shekara, ‘yan kwanaki bayan ya yi nasara kan Jake Paul a birnin Miami na Amurka ranar 19 ga Disamba.
Comments
No comments Yet
Comment