Sport
Dollar
40,9408
0.02 %Euro
47,6646
-0.12 %Gram Gold
4.395,8300
-0.25 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Kamfanin dillancin labaran Nijar ANP ya ruwaito cewa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta COLDEFF, Kanar Zennou Aghali Moussa, ne ya bayyana wannan a Yamai, babban birnin ƙasar.
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijar, COLDEFF, ta yi nasarar ƙwato takardar kuɗin FCFA 63,808,497,269 da kuma ƙadarori da suka kai FCFA biliyan biyar.
Kamfanin dillancin labaran Nijar ANP ya ruwaito cewa shugaban hukumar COLDEFF, Kanar Zennou Aghali Moussa, ne ya bayyana haka a ƙarshen mako a Yamai, babban birnin ƙasar.
Kanar Moussa ya yi wannan bayanin ne a gaban mambobin majalisar kare ƙasa (CNSP), kamar yadda kamfanin ANP ya ruwaito.
Da yake magana game da takardun da aka ce sun ɓace daga harabar hukumar tasa, Kanar Zennou Aghali Moussa ya ce babu gaskiya a cikin wannan maganar, yana mai cewa abin dariya ne.
Comments
No comments Yet
Comment