Sport
Dollar
41,9515
-0.14 %Euro
48,8020
-0.25 %Gram Gold
5.578,1900
0.08 %Quarter Gold
9.664,4100
-0.12 %Silver
65,8600
-0.39 %"An shafe illahirin unguwanni, sannan iyalai suna ta kara-kainar neman ruwa da wajen zama a cikin baraguzan," in ji UNRWA.
Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNRWA a ranar Alhamis ta ce akwai fiye da ton miliyan 61 na tarkace da baraguzai da suka lullube Gaza sakamakon yakin da Isra’ila ta shafe shekara biyu tana yi a yankin.
“An shafe illahirin unguwanni, sannan iyalai suna ta kara-kainar neman ruwa da wajen zama a cikin baraguzan,” kamar yadda UNRWA ta wallafa a shafin X.
Hukumar ta jaddada cewa aikinta na jinkai da ceton rayukan Falasdinawa na ci gaba a Gaza, duk da cewa har yanzu takunkuman Isra’ila na hana aiwatar da ayyukan jinkai na UNRWA
Shugaban UNRWA Philippe Lazzarini ya ce hukumar na da magunguna da mahimman abubuwan bukata da isasshen abinci na tsawon wata uku ga al’ummar Gaza.
A watan Oktoban 2024, majalisar dokokin Isra'ila, Knesset, ta kada kuri'ar amincewa da dakatar da ayyukan UNRWA a yankin Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye saboda zargin ma'aikatanta da hannu a hare-haren kungiyar Hamas ta Falasdinu a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Amma a ranar Laraba, Kotun Duniya ta yi watsi da ikirarin Isra'ila, tana mai cewa "Isra'ila ba ta tabbatar da zargin da ta yi cewa wani mahimmin bangare na ma'aikatan UNRWA 'yan Hamas ne" ko kuma suna da hannu a hare-hare ba.
Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa wajibi ne Isra'ila a karkashin yarjejeniyar Geneva ta amince da kuma sauƙaƙe shirye-shiryen agaji da kasashe uku da kungiyoyin agaji marasa son-rai, da suka hada da UNRWA da kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC), don tabbatar da cewa isasshen agaji ya isa Zirin Gaza.
Tun daga watan Oktoban 2023, yakin kisan kare dangi na Isra'ila ya kashe fiye da mutum 68,000 tare da jikkata fiye da 170,000, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza.
Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki ne a ranar 10 ga watan Oktoba a Gaza, bisa tsarin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar.
Comments
No comments Yet
Comment