Dollar

41,9554

-0.14 %

Euro

48,8170

-0.22 %

Gram Gold

5.536,4200

-0.66 %

Quarter Gold

9.664,4100

-0.12 %

Silver

65,4000

-1.08 %

Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya ya yi wasu manyan sauye-sauye a tsarin shugabancin hafsoshin tsaron Nijeriya da nufin karfafa tsarin tsaron kasar.

Shugaba Tinubu ya sauya Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya ya yi wasu manyan sauye-sauye a tsarin shugabancin hafsoshin tsaron Nijeriya da nufin karfafa tsarin tsaron kasar.

A sanarwar da mai taimaka wa Shugaban Kasa na musamman kan yada labarai, Sunday Dare ya fitar a ranar Jumma'a, an maye gurbin Babbaan Hafsan Hafososhin Nijeriya Janar Christopher Musa da sabon babban hafsa Janar Olufemi Oluyede, wanda shi ne Shugaban Sojin ƙasa a baya.

Haka kuma Shugaba Tinubu ya naɗa Manjo Janar W. Shaibu domin ya maye gurbin Oluyede, yayin da Air Vice Marshall S.K Aneke ya zama sabon hafsan sojin sama domin maye gurbin Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla.

Ita kuwa rundunar sojin ruwa, sabon hafsanta shi ne Rear Admiral I. Abbas inda ya maye gurbin Air Marshal Hasan Bala Abubakar

Sai dai ba a sauya Shugaban Rundunar Tsaro ta Leken Asiri ba, wato Manjo-Janar E.A.P Undiendeye.

A sanarwar, Shugaba Tinubu ya bayyana godiyarsa ga babban hafsan hafsoshin tsaro Janar Christopher Musa da sauran hafsoshin masu barin gado kan "aikin da suka yi cikin kishin kasa da sadaukarwa."

Sai kuma ya nemi sabbin hafsoshin tsaron da su yi aiki tukuru bisa amincewa da aka yi da su wajen dora musu alhakin wannan aiki, su kuma nuna kwarewa wajen shugabantar rundunar sojin Nijeriya.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#