Shugaban Turkiyya Erdogan ya ce halartar shugabannin duniya taron COP31 a Antalya shaida ce da ke nuna matakan da za a dauka kan sauyin yanayi da kuma kwarin gwiwar magance manyan kalubalen duniya.

Erdogan ya ce halartar shugabannin duniya COP31 zai ƙarfafa yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa jajircewar siyasar da shugabannin kasashe suka nuna a taron COP31 da ake kan gudanarwa a birnin Antalya, wata alama ce mai kyau wajen cim ma muradun yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi.

Erdogan ya yi kira da a ci gaba da wannan jajircewa domin tabbatar da cewa duniya ba ta wuce matakin dumamar yanayi na digiri 1.5 na ma'aunin Celsius ba.

“Jajircewar siyasar da aka nuna a Antalya abin karfafa gwiwa ne ga ayyukan da za a gudanar karkashin yarjejeniyar Paris. Mu ci gaba da wannan azama, mu kara kokarin aiwatar da alkawuran da aka dauka, tare da tabbatar da cewa burin takaita dumamar yanayi zuwa digiri 1.5 zai yiwu.” in ji Erdogan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis.

Erdogan ya kuma mika godiyarsa ga dukkan shugabannin kasashe da gwamnatocin da suka halarci taron, yana mai cewa haduwarsu da sakonnin da suka gabatar kai tsaye na da muhimmanci matuka a daidai lokacin da duniya ke fuskantar manyan kalubale.

Ya ce halartar shugabannin ya nuna jajircewar siyasa wajen yaki da sauyin yanayi, da kuma amincewa cewa za a iya shawo kan matsalolin duniya ta hanyar hadin gwiwa.

Shugaban na Turkiyya ya kuma gode wa kasashe, kungiyoyin kasa da kasa, bankunan raya kasa na bangarori daban-daban da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudummawar da suka bayar wajen nasarar taron.

Da yake tsokaci kan yadda yarjejeniyar Paris ta shekarar 2015 ta shiga shekaru goma da fara aiki, Erdogan ya ce tattaunawar da aka yi a taron ta sake tabbatar da cewa yaki da matsalar sauyin yanayi ba kawai ya rataya a wuyan kimiyya ba ne, har da nauyin da'a.

“Nauyin da ke kanmu ya shafi dukkan mutanen da tuni rayuwarsu ke fuskantar illolin sauyin yanayi, da al'ummomin da za su zo nan gaba, da kuma duniyar da rayuwar al'ummomi da tattalin arzikinsu suka dogara da ita,” in ji shi.

Fadada amfani da wutar lantarki da bunkasa masana'antu masu kare muhalli na cikin manyan muradun taron

Erdogan ya bayyana cewa tarukan manyan jami'an da aka gudanar a yayin taron sun ba da damar tattaunawa mai zurfi kan fadada amfani da wutar lantarki, da aiwatar da alkawuran sauyin yanayi, da bunkasa masana'antu masu kare muhalli, da karfin jure wa matsaloli, da kawar da shara da kuma samar da kudaden tallafin sauyin yanayi.

Ya ce tarukan sun kuma ba da muhimmanci ga bukatu da muradun Afirka, da yankin tekun Pacific da sauran sassan duniya, tare da jaddada bukatar aiwatar da matakan yaki da sauyin yanayi bisa la'akari da bukatun ci gaba da yanayin kowace kasa.

Yayin da ya tabo batun bala’o’in da suka faru a baya-bayan nan, wadanda suka yi sanadin asarar rayuka da kuma lalata hanyoyin samun abin dogaro, Erdogan ya ce wadannan al'amura sun nuna irin bukatar gaggauta daukar matakan kare bil'adama daga illolin sauyin yanayi.

Ya nuna goyon bayansa ga al'ummomin da bala'o'in suka shafa da wadanda ke taimaka musu wajen farfadowa, yana mai jaddada bukatar karfafa tsarin gargadin aukuwar bala'o'i da wuri, da kuma karfin jure wa barazanar, musamman a yankunan da suka fi fuskantar hadarin.

‘‘Dole wadannan batutuwa su ci gaba da kasancewa cikin manyan abubuwan da ake mayar da hankali a kansu, yayin da ake amfani da damarmakin da aka samu wajen fadada hanyoyin samun wutar lantarki, da bunkasa masana'antu masu kare muhalli da ci gaba mai dorewa suka samar,’’ in jiErdogan.

COP31: Taron da ya mayar da hankali kan aiwatar da alkawura

Erdogan ya ce taron ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da cewa kasashe da al'ummomin da suka fi bukatar tallafin kudi sun samu damar yin amfani da shi.

Ya bayyana cewa shirin Climate Implementation Bridge ya samu gagarumin goyon baya.

Ya ce shirin na da manufar mayar da alkawuran da aka riga aka dauka zuwa ayyuka na zahiri, ta hanyar karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe, da cibiyoyin hada-hadar kudi da kuma sauran masu ruwa da tsaki, tare da tallafa wa shirye-shiryen da kasashe suka tsara kan sauyin yanayi, da karfin jure wa matsaloli da ci gaba mai dorewa.

‘‘An tsara COP31 ne a matsayin taron da zai mayar da hankali kan aiwatar da alkawura da aka dauka,’’ a cewar Erdogan yana mai kari da cewa yana mai maraba da goyon bayan da aka bai wa shirin ‘‘35x35 Global Electrification Pledge.’’

Ya ce shugabannin kasashe da dama sun bayyana damarmakin da fadada amfani da wutar lantarki ke samarwa yayin taron, inda kasashe da dama suka riga suka shiga shirin.

Ya kara da cewa fadada amfani da wutar lantarki bisa la'akari da bukatu da abubuwan da kowace kasa ta sanya a gaba na iya taimakawa wajen tabbatar da tsaron makamashi da bunkasa tattalin arziki.

Erdogan ya ce, jagorancin Turkiyya a COP31 ya yi kokarin kara muhimmancin siyasa ga batun aiwatar da alkawura, tare da hada gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da mafita ta zahiri.

Kazalika ya bayyana fatan cewa, gagarumar gudummawar da shugabancin Turkiyya zai bari ita ce karfafa hadin gwiwa tsakanin wadanda ke tsara manufofin kasashensu da wadanda ke taimakawa wajen aiwatar da su, yayin da ake ci gaba da kokarin tabbatar da yarjejeniyar Paris.

TRT Afrika — TRT Afrika

Hoto: АА

#