Dollar

42,0751

0.17 %

Euro

48,7444

0.06 %

Gram Gold

5.447,8700

0.32 %

Quarter Gold

9.212,2300

0 %

Silver

66,2200

0.28 %

Rahotanni daga Barcelona na cewa Victor Osimhen ya shiga sahun 'yan wasan da ta zayyana don maye gurbin Robert Lewandowski, wanda zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar bana.

Da gaske ne Barcelona za ta nemi Victor Osimhen don maye gurbin Robert Lewandowski?

Tauraron ɗan wasa ɗan asalin Nijeriya, Victor Osimhen ya fara samun zawarci daga Barcelona, wadda ke shirin maye gurbin Robert Lewandowski ɗan asalin Poland,

Mai shekaru 37, Lewandowski bai samu sabuwar kwantiragi ba ƙarƙashin koci Hansi Flick, wanda a yanzu rahotanni ke cewa ya kama hanyar neman wanda zai gaje lambar Lewi.

A ƙarshen kakar bana ne ake tunanin Lewandowski zai bar Barca, wanda zai tilasta wa Barca neman wani zaƙaƙurin ɗan wasan gaba mai ciyo ƙwallo.

Sai dai shi kuma Victor Osimhen a bazarar bana ne ya koma Galatasaray bayan barin Napoli ta Italiya, duk da gabanin nan ya buga wa ƙungiyar ta Turkiyya wasa a matsayin ɗan-aro.

Osimhen dai ba ya ɓoye aniyarsa ta buga wasa a ɗaya cikin manyan lig-lig na Turai biyar ba, ciki har da Firimiya ta Ingila da LaLiga ta Sifaniya, inda Barcelona ke cikin manyan ƙungiyoyi.

Tsadar Osimhen

A bazara mai zuwa ne rahotanni daga shafin Mundo Deportivo ke cewa Barca za ta gwada sa’ar zargo Osimhen daga Turkiyya.

Osimhen ya ci ƙwallaye 37 a wasanni 41 a kakarsa ta farko a Galatasaray, wanda wata ƙarin hujja ce ta ƙwarewarsa. Sannan yana da kwantiragin shekara huɗu ne a Galatasaray.

A Fabrairu aka tsawaita kwantiragin Lewandowski zuwa 30 ga Yunin 2026, bayan da a kakar bara ya ci ƙwallaye 42 a wasanni 52. Akwai raɗe-raɗin cewa Lewi zai yi ritaya bayan barin Barca.

A yanzu dai babban ƙalubalen da ke gaban Barcelona shi ne iya biyan maƙudan kuɗin ɗauko Osimhen, wanda shi ne ɗan wasan da ya fi kowa ɗaukar albashi a gasar Super Lig ta Turkiyya.

Albashinsa ya kai dala miliyan $17.5 a shekara, ga ƙarin dala miliyan $7 na bonos, baya ga cewa Galatasay sai da ta zuba dala miliyan $88 wajen sayo shi. 

A fili take cewa Barcelona na cikin ƙangin rashin kuɗi tsawon shekaru, sannan akwai wasu taurarin ‘yan wasan da za ta iya ɗauka kamar su Harry Kane daga Bayern Munich, ko Erling Haaland daga Manchester City.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#