Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Lamine Yamal zai sayi gidan tsohon ɗan-wasan Barcelona gerard Pique, wanda ya zauna shi da tsohuwar matarsa, Shakira kafin aurensu ya rabu.
Matashin ɗan-wasan Barcelona, Lamine Yamal ya shirya tsaf don sayan gidan da tsohon ɗan-wasan Barcelona, Gerard Pique ya zauna shi da tsohuwar matarsa, shahararriyar mawaƙiya, Shakira wadda suka rabu a 2022.
Katafaren gidan ya kai dala miliyan 16, kuma yana da gidaje uku, da ramin ninƙaya da filin tenis da ɗakin ɗaukar bidiyo da murya.
Idan Yamal wanda ɗan Sifaniya ne, ya sai gidan ya shiga da budurwarsa, mawaƙiya 'yar Argentina, Nick Nicole wadda ta girmi Yamal da shekara 7, hakan zai yi kama da abin da Pique ya yi, wanda shi ma ɗan Sifaniya ne, kuma Shakira 'yar Columbia ta girme shi da shekara 10.
Yamal na tashen farin jin da samun kuɗi daga sabuwar kwantiragin da ya sanya hannu da Baraca zuwa 2031. Sannan yana samun kuɗin talla.
A baya dai, matasin ɗan-wasan ya saya wa mahaifiyarsa da kakarsa gida, kuma ya taɓa cewa yana rayuwa ne tare da mahaifiyarsa a gida guda.
A yanzu da ya kai shekara 18, akwai yiwuwar ya koma rayuwa da budurwarsa, Nicole wadda ta zamo mai muhimmanci a rayuwarsa a halin yanzu.
Comments
No comments Yet
Comment