Dollar

41,3835

0.02 %

Euro

48,7952

0.32 %

Gram Gold

4.942,9700

0.81 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban ƙasar Turkiyya Erdogan ya bayyana fatansa kan cewa ƙarin samun masu amincewa da Falasɗinu zai sa a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar kafa ƙasashe biyu masu 'yancin kansu.

Batun kisan gillar Isra'ila a Gaza zai kasance babbar ajandata a Taron MDD: Erdogan

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce jawabin da zai gabatar a zauren Majalisar Dinkin Duniya zai mayar da hankali ne kan kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, inda ya yi kira da a ɗauki matakin gaggawa don kare Falasɗinawa da kuma ciyar da yarjejeniyar ƙasashen biyu gaba.

Da yake jawabi a filin jirgin saman Ataturk na Istanbul kafin ya tashi zuwa birnin New York a ranar Lahadi, Shugaba Erdogan ya ce, "A cikin jawabina a Majalisar Dinkin Duniya, zan yi tsokaci kan yanayin da ake ciki a Gaza, da kuma ƙoƙarin Turkiyya na kare zaman lafiya a yankin."

Ya ce taron UNGA na bana zai sha bamban da na baya, saboda "ƙasashe da dama za su amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa".

Bayan ya isa cibiyar Turkevi da ke New York, Erdogan ya shaida wa manema labarai cewa ganawar da zai yi da shugaban Syria Ahmed al Sharaa a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya, da kuma shugaban Amurka Donald Trump a Washington, na da matuƙar muhimmanci saboda "sun shafi batun yankin."

"A gare mu, kowane mataki da aka ɗauka a Gabas ta Tsakiya yana da matuƙar muhimmanci, kuma ba shakka, muna buƙatar mu tattauna waɗannan batutuwa da Shugaba Trump," in ji shi.

Shugaban ya bayyana fatansa na cewa, ci gaba da amincewa da Falasɗinu, zai sa a ‘‘gaggauta aiwatar da shawarwarin samar da ƙasashen biyu,’’ ya kuma ƙara da cewa batun hakki da tsaron 'yan Turkiyya da ke Cyprus ma zai kasance cikin ajandarsa.

Erdogan ya ce zai gana da Trump a yayin taron domin tattaunawa kan batun haɗin gwiwa kan kasuwanci da masana'antar tsaro, yayin da ya jaddada cewa "tsarin MDD a halin yanzu bai isa ya sauke nauyin da ke kansa ba".

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#