Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru da tsakar dare kafin kwanciyar hankali ya dawo

An ji harbe-harbe da fashe-fashe a yankin Tahoua na Nijar

Mazauna yankin Tahoua a Jamhuriyar Nijar sun ce sun ji ƙarar harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa masu ƙarfi a daren Lahadi, lamarin da ya tayar da hankalin jama’a kafin daga bisani kwanciyar hankali ya dawo.

Rahotanni sun nuna cewa an ji karar harbe-harben ne da misalin karfe 3:00 na dare agogon ƙasar, inda mazauna yankin suka ce an kuma ji wasu fashe-fashe masu ƙarfi.

Wani mazaunin garin Tahoua ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa maharan da ba a tantance ko su wane ne ba sun zo ne a kan babura.

Ya ce an yi musayar wuta tsakanin maharan da jami’an tsaro a hanyar da ta nufi filin jirgin saman birnin da kuma wasu sassan tsakiyar garin.

Sai dai wani mazaunin garin ya bayyana cewa kafin fitowar alfijir an daina jin ƙarar harbe-harben kuma lamarin ya lafa.

Har zuwa safiyar Litinin babu wani cikakken bayani kan ko akwai waɗanda suka rasa rayukansu ko suka jikkata sakamakon harin.

Jamhuriyar Nijar ta shafe kusan shekaru goma tana fama da hare-haren ƙungiyoyin ta’adda masu alaƙa da Al-Qaeda da kuma Daesh.

Lamarin na Tahoua ya faru ne ’yan makonni bayan wani hari da ake zargin mayaƙan Daesh sun kai kan babban filin jirgin saman ƙasar da ke birnin Yamai.

A makon da ya gabata ma, an kashe wani jami’in kwastam tare da aƙalla fararen hula uku a wani hari da aka kai wani shingen binciken ababen hawa kusa da iyakar Nijeriya a yankin Tahoua.

Yankin Tahoua na daga cikin wuraren da ’yan fashi da makami da masu safarar haramtattun kayayyaki ke amfani da su wajen zirga-zirga.

Tushen labari: Newstimehub

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#