Sport
Dollar
41,0593
0.04 %Euro
48,0223
0.33 %Gram Gold
4.484,7400
0.04 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A watan Afrilu ne Joseph Oloyede ya amsa laifinsa na tuhumar da ake masa cewa ya karbi kuɗaɗe na shirin tallafi ga ƙananan 'yan kasuwa a lokacin annobar cutar covid-19.
An yanke wa wani sarki daga yankin Yarabawa a Nijeriya hukuncin zaman gidan yari na shekaru hudu a Amurka saboda jagorantar wata maƙarƙashiya don amfana da shirye-shiryen rancen gaggawa na annobar cutar COVID-19 da aka samar domin taimakon masu ƙananan kasuwanci.
Joseph Oloyede, mai shekaru 62, ya amsa laifinsa a watan Afrilu kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki don aikata zamba ta hanyar sadarwa da kuma yin mu'amala da kudaden da aka samo ta haramtacciyar hanya.
A ranar Talata, wani Alkalin Kotun Gunduma ta Amurka ya yanke masa hukuncin zaman gidan yari na watanni 56, kamar yadda Ofishin Lauyan Gwamnatin Amurka na Gundumar Arewa ta Ohio ya bayyana a wata sanarwa.
Oloyede yana da shaidar zama ɗan ƙasashe biyu, Nijeriya da Amurka, kuma yana zaune a Medina, Ohio. Haka kuma, yana rike da mukamin sarki na gargajiya a garin Ipetumodu da ke jihar Osun a Nijeriya.
Ba da gida
“Haka kuma, ya rasa gidansa da ke Medina a Foote Road, wanda ya saya da kudaden da ya samu daga wannan zamba,” in ji sanarwar.
Comments
No comments Yet
Comment