Sport
Dollar
43,2789
0.22 %Euro
50,2002
-0.1 %Gram Gold
6.375,3800
-0.3 %Quarter Gold
10.664,4800
0.75 %Silver
124,3300
-2.65 %Rundunar 'yansandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta tabbatar da kisan wata mata mai suna Fatima Abubakar da 'ya'yanta shida a a unguwar Dorayi Charanchi da ke cikin birnin Kano
Rundunar ’Yansandan Nijeriya Reshen Jihar Kano ta kaddamar da bincike kan wani mummunan hari da aka kai wa wata mata da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Charanchi da ke cikin birnin Kano, lamarin da ya yi sanadin mutuwar matar da ‘ya’yan nata.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:10 na rana a ranar 17 ga Janairun 2025, lokacin da ’yan sanda suka karɓi kiran gaggawa da ke nuna cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidan Haruna Bashir a unguwar Dorayi Charanchi.
‘Yansandan sun ce a yayin harin, ana zargin maharan da amfani da muggan makamai wurin aikata wannan ta’asar.
Rundunar ‘yansandan ta ce mahaifiyar yaran da aka kashe sunanta Fatima Abubakar mai shekara 35. Sun samu munanan raunuka a yayin harin, kuma an garzaya da su zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
Bayan samun rahoton, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya gaggauta tura tawagar ’yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, kamar yadda sanarwar da ‘yansandan suka fitar ta bayyana.
Tawagar ta kasance karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Ayyuka, DCP Lawal Isah Mani, domin tabbatar da tsaron yankin da kuma fara binciken farko.
Kwamishinan ’Yan Sandan ya kuma umarci Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID), ACP Wada Jarma, da ya jagoranci cikakken bincike domin ganowa tare da kama waɗanda ke da hannu a harin.
Comments
No comments Yet
Comment