Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Abba Atiku Abubakar, ɗa ga tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya shiga Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.

Abba Atiku Abubakar ya shiga Jam'iyyar APC

Abba Atiku Abubakar, ɗa ga tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya shiga Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.

A wani saƙo ta shafin Facebook da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Nijeriya Barau Jibrin ya fitar, ya yaɗa hotunan da ke nuna ɗan gidan Atiku da ‘yan tawagarsa na karɓar jam’iyyar ta APC.

Sanata Barau ya ce “Yau a zauren Majalisar Dattawa ta ƙasa, a hukumance na karɓi Abubakar (Abba) Atiku Abubakar, ɗan tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar zuwa babbar jam’iyyarmu ta APC.”

Sanatan mai wakiltar mazabar Kano ta Arewa ya ci gaba da cewa ya karɓi Abubakar a gaban masu ruwa-da-tsaki da dama na jam’iyyar da suka haɗa da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na shiryyar Arewa Maso-Gabas Kwamared Mustapha Salihu, mai taimaka wa shugaban ƙasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Mohmoud Abdullahi, dattijo Malam Hamza Darma da sauran su.

“A mataki na tarihi da jarumta, Abba (Abubakar) ya sanar da murabus daga jam’iyyar PDP, ya bayyana cikakkiyar aniyarsa ta mara wa APC baya da sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027,” in ji Barau.

A jawabinsa, Abba Atiku ya ce ya ziyarci majalisar ne don bayar da sanarwa a hukumance cewar ya bar jam’iyyar PDP tare da shiga APC saboda kyakkyawan jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin.

“Tare da wannan ci-gaba, zan yi aiki tare da Sanata Barau don tabbatar da nasarar wa’adi na biyu na Shugaba Tinubu a 2027. Ina umartar dukkan jami’aina da mambobin ƙungiyata ta Haske Atiku da a yanzu ta koma Haske Tinubu da su shiga APC, kuma su yi aiki don ta-zarcen Shugaba Tinubu,” Abba Atiku Abubakar ya faɗa wa dandazon jama’ar da ke wajen.

A ƙarshe Sanata Barau ya shaida wa Abba da magoya bayansa cewa za su samu dukkan goyon bayan da suke so a jam’iyyar APC.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#